Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages



 


Breaking News:

latest

Wa Zai Kare Bayin Allah A Kano Daga 'Yan Daba Masu Kwacen Waya, Yayin Da Kamfen Ya Matso?

Daga Al-Amin Ciroma Kwacen waya a Jihar Kano da 'yan daba ke aikatawa ba sabon labari ba ne, sai dai lamarin na kara kazancewa a kullum ...




Daga Al-Amin Ciroma


Kwacen waya a Jihar Kano da 'yan daba ke aikatawa ba sabon labari ba ne, sai dai lamarin na kara kazancewa a kullum yaumin, inda mafi yawa, bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba suke fadawa a ciki. 


Rahotanni da dama na bayyana yadda 'yan daban ke kai wa mutane hari, a wasu lokutan ma, har su rasa rayukansu sakamakon munanan hare-haren matasan.


Wannan matsalar, kamar yadda TNL HAUSA ta gudanar da bincike mai zurfi, ta haifar da wata babbar tambaya, musamman yayin da harkokin siyasa ke kara É—aukar zafi gabanin zaÉ“en 2027. 


Tambayar dai ita ce; Shin me zai faru idan 'yan daban suka cakuda da gangamin siyasa?


Wakilinmu ya fada mana cewa Kano na da dogon tarihi kan wannan bahallatsar, musamman a lokutan yakin-neman-zabe, inda a mafi yawan lokuta ake amfani da wasu ƙungiyoyin matasa 'yan daba, domin tsorata abokan hamayya, a yayin gumurzun neman zabe.


A baya-bayan nan ma, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari kasuwar Waya ta Farm Centre a Kanon, a wani taron siyasa, inda da dama wasu bayin Allah da ke kasuwanci a wajen suka rasa manyan kadarorinsu.


Ba nan kadai lamarin ya tsaya ba, sai da rahotanni suka tabbatar da rasa rayuka kusan mutum Shida. Lamarin da hukumar 'yan sanda ta tabbatar, ta kama wasu mutane tare da yin alƙawarin ci gaba da bincike kan harin.


Binciken da TNL HAUSA ta gudanar, ya nuna a fili cewa babban hatsarin da talakawa da saurin bayin Allah da su da hannu a siyasa, a bayyane yake.


Alal-misali, dan kasuwa na iya fadawa cikin homar fusatattun matasan, a yayin da yake kokarin bude shagonsa, ko gudanar da harkokin kasuwancinsa.


Dalibi na iya kasancewa yana komawa gida, ko Fasinja da ke tafiyar da harkokin zirga-zrigarsa, dukkaninsu ba lallai su kasance masu sha'awa, ko masu ruwa da tsaki a harkar siyasa, a daidai lokacin da ake yin taron ba, amma idan ba a yi sa'a ba, su samu kansu cikin mummunan tashin hankali da zarar matasan sun yi arangama da su.  


TNL HAUSA ta zayyano wasu manyan tambayoyi kamar haka:

Su waye masu daukar nauyin waÉ—annan matasan da ke yawo a cikin tarukan siyasa?

Shin ko su ma magoya bayan jam'iyyun ne na gaskiya?

Ko kuma su ma masu ruwa da tsaki ne a harkar siyasar?


Wadannan tambayoyi ne da ya kamata jam'iyyun siyasa da hukumomin tsaro, su amsa su, kafin tsunduma cikin harkar yakin neman zaben 2027.


Babban abin da ake gudu shi ne, dabar siyasa a yau na iya zama ta'addanci. Haka kuma, matashin da aka yo hayarsa domin tsoratar da abokan hamayyar siyasa a yau, zai iya gano cewa tashin hankali ya fi masa saukin samun kudi fiye da aikin Halal.


A yayin gudanar da wannan binciken, TNL HAUSA ta nemi jin dalilan da ke sa matasa shiga irin haramtattun hanyoyin aikata barna?

Amsar ba mai sauÆ™i ba ce. 


Domin wasu za su ce rashin aikin yi, ko shaye-shayen Æ™wayoyi, ko talauci, ko abota da miyagu, ko kuma uwa uba, rashin kulawar iyaye, amma anya rashin wadannan, ko rashin aikin yi na iya zama hujja ta aikata laifi? 


Binciken ya tabbatar cewa mafi yawan matasan Kano mutane ne masu kokari, masu neman na kansu, kuma masu son yin rayuwa cikin mutunci da bin doka da oda.


Amma babban abin da ke ci wa al'umma tuwo-a-kwarya shi ne yadda aka yi sakaci, aka zura idanu 'yan daba ke cin karensu-ba-babbaka!


A irin wannan yanayi, me ya kamata gwamnati ta yi? Haka ma wace irin rawa, ya kamata hukumomi su yi, ba sai kawai su rika jira sai an kashe mutane, ko aikata barna, sannan su ce za su dauki mataki ba.


Abin da ya kamata a yi shi ne gano wuraren da 'yan dabar ke sheke-ayarsu, suke aikata barna, su gudanar da cikakken bincike kan hanyoyin da ake bi wajen safara, da sayar da wayoyin da aka sata, tare da tarwatsa kasuwannin da ke karɓar irin waɗannan kayayyaki.


Haka kuma, a kafa wa 'yan siyasa tsauraran dokokin tabbatar da cewa ba su yi hayar 'yan daba ba. Su nemar wa kansu hanyoyin da za su bi, yayin gudanar da gangamin neman zabe, tare da tsare-tsaren masu inganci, kafin a ba su damar gudanar da manyan taruka, ko gangami.


Bai kamata a bar mutanen da aka san suna da halin tashe-tashen hankula, su mayar da tarukan siyasa wata damar zaluntar al'umma ko aikata manyan laifuka ba.


Don haka, ya zama wajibi gwamnati ta tunkari tushen matsalar ta hanyar samar da ayyukan yi na gaskiya, koyar da sana'o'i da kuma shirye-shiryen gyara halayen matasan da ke cikin hadarin shiga aikata manyan laifuka.


TNL HAUSA na ganin cewa al'ummar Kano ba za ta lamunci barin 'yan daba na aikata laifuka da rana tsaka ba, musamman ma a wannan lokuta na siyasa. Ba daidai ba ne a kyale 'yan daba su mayar da cibiyoyin kasuwanci wuraren da akata ta'addanci da rashin rayuka ba.


Kowa dai ya san cewa Siyasar gaskiya, ba ta bukatar tashin hankali ko harkar Daba. Dimokuradiyya ce mai ba wa kowa 'yancin bayyana ra'ayinsa.


Wakilinmu ya ce, rahoton kisan wani matashin É—an kasuwa, mai shekaru 25 Mallam Abdulmalik a jiya Alhamis a kan titin birnin Kano, kamar yadda TNL HAUSA ta ruwaito, lamari ne mai ban takaici da alhini. 


Wane takamaiman mataki aka dauka, shi ke nan an rasa Abdulmalik, gobe kuma sai wa?

Ko kadan babu adalci idan har lamarin ya ci gaba da tafiya a haka!

No comments