Breaking News

Shinkafi Ya Buƙaci INEC Ta Cire Sunan Ya’u, Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Zaben Fitar Da Gwani Na APC

Daga Abdullahi Alhassan 

Wani jigo a jam’iyyar APC, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta cire sunan Sanata Sahabi Alhaji Ya’u daga jerin sunayen ’yan takarar jam’iyyar na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa a zaɓen 2027.

Shinkafi, wanda shi ma ke neman takarar kujerar, ya ce ci gaba da sanya sunan Sanata Ya’u a matsayin ɗan takarar APC ya saɓa wa hukuncin kotu da ya soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazabar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Shinkafi ya bayyana cewa INEC na fuskantar barazanar rasa amincewar jama’a idan ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula da hukuncin kotuna.

Ya ce wallafa sunan ɗan takarar duk da hukuncin kotunan da suka saurari shari’ar na iya raunana martabar ɓangaren shari’a da kuma amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.


Rikicin ya samo asali ne daga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, wadda Mai Shari’a Hassan Dikko ya yanke a ranar 31 ga Agusta, 2026, inda ya soke zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a ranar 19 ga Mayu, 2026.

Kotun ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne ba tare da bin tanade-tanaden dokar zaɓe da ƙa’idojin jam’iyyar ba, don haka babu ɗan takara ingantacce da ya samu nasarar zaɓen.

Bayan rashin gamsuwa da hukuncin, Sanata Ya’u ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Sakkwato domin ƙalubalantar hukuncin.

Sai dai a ranar 20 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Abubakar M. Talba ya yi watsi da ƙarar mai lamba CA/S/239/2026, yana mai bayyana ta a matsayin wadda ba ta da ingantaccen dalilin da zai sa a amince da ita.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta kuma tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya tare da umartar APC da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani, wanda zai ƙunshi dukkan ’yan takarar da aka tantance a mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa.

Dakta Shinkafi ya ce abin mamaki ne yadda hukumar zaɓen ke ci gaba da nuna sunan Sanata Ya’u a matsayin ɗan takarar APC, duk da hukuncin kotunan biyu.

Ya buƙaci hukumar da ta yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da bin doka, dawo da amincewar jama’a da kuma kare mutuncin tsarin zaɓe a Nijeriya.

Sai dai Dakta Shinkafi ya kuma yi zargin cewa ci gaba da riƙe sunan Sanata Ya’u wani shiri ne da ake ƙoƙarin aiwatarwa domin hana APC samun ɗan takara a Zamfara ta Arewa, kamar yadda ya ce ta faru a wasu zaɓukan baya a jihar.

Ya tuna da zaɓen 2019, lokacin da Kotun Ƙoli ta soke zaɓukan fidda gwani na APC a Zamfara, abin da ya sa jam’iyyar ta rasa kujeru da dama ga ’yan takarar da suka zo na biyu.


“Ba za mu bari a maimaita irin wannan yanayi ba,” in ji Dakta Shinkafi


Ya ƙara da cewa ya umarci lauyoyinsa da su rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban INEC domin tunatar da hukumar hukuncin kotunan da kuma umarnin sake gudanar da zaɓen fidda gwani.

A wata wasiƙar mai kwanan wata 27 ga Oktoba, 2026, wadda lauyan Shinkafi, S.Y. Aliyu na kamfanin lauyoyi na Yas Law Firm, ya sanya wa hannu, lauyoyin sun buƙaci INEC da ta dakatar da wallafa sunan Sanata Ya’u har sai an sake gudanar da zaɓen fidda gwani ko kuma Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe idan an ɗaukaka ƙara zuwa gare ta.

Lauyoyin sun bayyana cewa wallafa sunan kowane ɗan takara kafin kammala zaɓen fidda gwani da kotu ta bayar da umarni a sake gudanarwa na iya saɓa wa tsarin shari’a da dokokin zaɓe.

No comments