NUJ Ta Yi Allah-Wadai da Fashin da Aka Yi A Horizon FM Dutse
Daga Hadi Bawa
Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa, ta yi Allah-wadai da harin fashi da makami da aka kai gidan rediyon Radio Nigeria Horizon FM da ke Dutse, wanda ya yi sanadin sace wasu kayayyaki, lalata tiransifoma da jikkata wasu ma’aikata.
TNL Hausa ta jiwo cewa, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan lamarin, tare da buƙatar gwamnatin jihar Jigawa da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kare kafafen yaɗa labarai daga irin waɗannan hare-hare.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NUJ na jihar, Kwamared Isma’il Ibrahim Dutse da Sakataren ƙungiyar, Kwamared Aminu Umar Shuwajo, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa saƙon jaje ga Babban Manajan tashar, Alhaji Habibu Nuhu Kila, da sauran ma’aikatan da abin ya shafa. Ta kuma yi wa waɗanda suka samu raunuka fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa maharan sun shafe sama da sa’o’i huɗu suna gudanar da harin cikin dare, inda suka ɗaure wasu ma’aikata da igiyoyi domin hana su ihu ko neman taimako.
Daga cikin kayayyakin da aka lalata akwai tiransifomar tashar da igiyoyin lantarki baya ga wasu kadarorin da aka lalata.
Ɓarnar da aka yi ta bayyana ne lokacin da kwamitin gudanarwa na NUJ na jihar ya kai ziyarar jaje tashar.
A yayin ziyarar, Babban Manajan ya nuna wa tawagar irin asarar da aka tafka, wadda ake hasashen ta kai miliyoyin nairori. Haka kuma, za a buƙaci kashe kuɗaɗe masu yawa wajen gyara da sauya kayan aikin da suka lalace.
NUJ ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa tashar wajen shawo kan matsalolin da harin ya haifar, tare da samar da ingantaccen tsaro ga gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai a faɗin jihar.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro su ƙara kaimi wajen gudanar da bincike, gano waɗanda suka aikata laifin, cafke su da kuma gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Ta jaddada cewa ya zama wajibi a ƙarfafa tsaron kafafen yaɗa labarai, musamman a wannan lokaci da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi.
A ƙarshe, NUJ ta yi addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga ma’aikatan da suka jikkata, tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya maye wa tashar da ma’aikatanta asarar da suka yi.


No comments