Breaking News

NCA ta bukaci a binciki bidiyon da ke barazanar kashe Kiristoci a Enugu da Jos



Daga Hauwa’u Maikudi

Ƙungiyar Kiristocin Arewa (NCA) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin wasu matasa na barazanar kashe Kiristoci a Enugu da Jos.

Shugaban ƙungiyar, Rev. (Dr.) Joseph John Hayab, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television a ranar Laraba.

Hayab ya ce yana da muhimmanci hukumomi su tabbatar da sahihancin bidiyon, tare da gano ko an yi masa kwaskwarima da kuma dalilan da suka sa aka yi hakan.

Ya ƙara da cewa idan barazanar da ke cikin bidiyon ta tabbata gaskiya ce, ya kamata a hukunta waɗanda suka yi ta bisa doka.

Shugaban NCA ya kuma yi gargaɗi kan yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, yana mai cewa bai kamata a mayar da batun abin ce-ce-ku-ce da zai iya ƙara rura wutar ƙiyayyar addini ba.

Ya ce ya kamata a gudanar da binciken cikin gaskiya, duba da yadda lamarin zai iya shafar tsaron ƙasa, zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da kuma zaman tare a Najeriya.

No comments