Breaking News

Saudiyya Ta Yi Wa Marasa Lafiya Aiki Kyauta A Kano

Daga Aliyu Saleh 

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin tallafin kiwon lafiya da gwamnatin Saudiyya ta ɗauki nauyi a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), inda aka yi wa marasa lafiya 52 aikin tiyata kyauta a fannin cututtukan mafitsara da hanyoyin fitsari cikin kwanaki shida.

Ƙungiyar ƙwararrun likitoci daga Saudiyya ce ta gudanar da aikin ƙarƙashin Cibiyar Sarki Salman ta Tallafin Agaji da Ceto, inda aka fi mayar da hankali kan marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ba za su iya biyan kuɗin irin wannan aikin tiyata na musamman ba.

Da yake jawabi a wajen rufe shirin ranar Juma’a, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa gwamnatin Saudiyya da ƙungiyar likitocin bisa taimakon da suka bayar wajen kula da mazauna jihar da ke buƙatar kulawar lafiya ta musamman. 

Ya ce wannan shi ne karo na huɗu da ƙungiyar likitocin Saudiyya ta gudanar da irin wannan aikin tiyata kyauta a Kano.

Gwamnan ya yi tilawar cewa a shekarar 2023, an yi wa fiye da mutane 2,300 aikin tiyatar ido kyauta a jihar ƙarƙashin irin wannan haɗin gwiwa. 

Ya ƙara da cewa wasu tagwaye da aka haifa a Kano a haɗe an kai su Saudiyya a shekarar 2023 domin yi musu aikin tiyata na musamman, inda suka shafe shekaru biyu suna samun kulawar lafiya kafin su dawo jihar.

Yusuf ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da Saudiyya a fannin kiwon lafiya, yana mai cewa ana shirye-shiryen fara gudanar da ayyukan tiyatar zuciya a Kano. 

Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari wajen inganta kayayyakin more rayuwa na kiwon lafiya, ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya da faɗaɗa damar samun ayyukan jinya da tiyata na musamman.

Gwamnan ya yaba wa hukumar gudanarwa da ma’aikatan AKTH bisa jajircewarsu wajen inganta harkokin kiwon lafiya, tare da godiya ga Jakadan Saudiyya a Najeriya da Jakadan Ƙasar Saudiyya na Kano, Sheikh Khalil Ahmad, kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin Kano da Saudiyya.

Shugaban tawagar likitocin, fitaccen likitan cututtukan mafitsara, Dr. Ali Ibn Mahfouz, ya ce tawagar ta ƙunshi ƙwararrun likitoci da suke da gogewa, waɗanda suka gudanar da ayyukan tiyatar da ake buƙata cikin nasara ba tare da samun wata matsala ba. 

Ya ce nasarar aikin ta samo asali ne daga ƙwarewar likitocin da kuma kyakkyawan haɗin gwiwar ma’aikatan lafiya na AKTH.

No comments