Abin Da Ya Sa Na Fice Daga APC Na Koma NDC -Jigo A Siyasar Jihar Zamfara
Daga Hadi Bawa
Wata jigo a APC a Jihar Zamfara, Hadiza Liman, ta fice daga jam’iyyar tare da magoya bayanta zuwa NDC.
TNL HAUSA ta jiwo cewa, Liman ta sanar da sauya sheƙar ne ranar Juma’a yayin da take zantawa da manema labarai a gidanta da ke Gusau, babban birnin jihar.
Ta ce ta ɗauki matakin ne saboda abin da ta bayyana a matsayin rashin kulawa daga Gwamna Dauda Lawal, duk da cewa ita da magoya bayanta sun mara masa baya a lokacin da ya samu nasarar zama gwamnan jihar a shekarar 2023.
Liman ta ce: “Tun lokacin da muka bi Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC, Gwamna Dauda Lawal bai kula da mu ba.”
Ta kuma bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara na NDC, Sanata Kabiru Garba Marafa, gabanin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
Sai dai, kalaman Liman game da rashin kulawa daga gwamnan ra’ayi ne da ta bayyana a matsayin dalilin sauya sheƙarta, ba wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar mana da wannan ra'ayin nata.
A wani taro da ta gudanar da magoya bayanta, Hadiza Liman ta sha alwashin rama abin da aka yi mata, tana mai cewa ana yin siyasa ne don a samu, amma ita ba gani a ƙasa ba.
Duk ƙoƙarin da Wakilinmu ya yi don jin ta bakin ɓangaren Gwamna Dauda Lawal a kan wannan iƙirarin haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.


No comments