Kotu Ta Aika Da Matar Da Ta Kashe Mijinta Saboda Zai Kara Aure Gidan Yari A Kano
Daga Hadi Bawa
Kotun Shari’a da ke yankin Post Office a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wata mata mai suna Bilkisu Sani Rogo a gidan yari, bisa zargin kashe mijinta, Malam Hamisu, a Bakin Kasuwa da ke Ƙaramar Hukumar Rogo ta jihar.
TNL HAUSA ta samu bayanin cewa an gurfanar da Bilkisu a gaban kotun ne bisa zargin kashe mijinta bayan ta samu labarin cewa yana shirin ƙaro mata abokiyar zama.
A yayin zaman kotun, wanda Alƙali Garba Hamza Malafa ya jagoranta, mai gabatar da ƙara, Barista Awaisu, ya gabatar da zarge-zargen da ake yi wa Bilkisu.
Sai dai wadda ake zargin ta musanta cewa ita ce ta kashe mijinta.
Bayan sauraron bayanan da aka gabatar a gabanta, kotun ta bayar da umarnin a tsare Bilkisu a gidan yari.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026.


No comments