Breaking News

Rundunar Sojan Ruwa Ta Kaddamar Da Ayyukan Raya Al'umma



Daga Zainab Idris Bamalli

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta kaddamar da wasu muhimman ayyukan raya al'umma a yankin Uzoubi-Umuna da ke ƙaramar hukumar Orlu a jihar Imo, da nufin inganta rayuwar al'umma da ƙarfafa zaman lafiya da tsaro.

Ayyukan sun haÉ—a da gyaran babban É—akin taron jama'a na Okwu Owerre Civic Hall, wanda aka fi sani da Obi Okonko, da kuma samar da matattarar ruwa mai É—aukar lita dubu goma, tare da bututun rarraba ruwa da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana.

An gudanar da ayyukan ne ƙarƙashin shirin rundunar na Special Intervention Quick Impact Project Scheme, wanda aka tsara domin taimaka wa al'umma ta hanyar ayyukan ci gaba.

Yayin bikin kaddamar da ayyukan, Babban Hafsan Sojin Ruwa na Najeriya, Mataimakin Admiral Idi Abbas, wanda Babban Daraktan KuÉ—i da Kasafin KuÉ—i na rundunar, Rear Admiral Omoyola Olukoya, ya wakilta, ya bayyana cewa rundunar ta fahimci muhimmancin samar da ci gaba mai É—orewa a cikin al'umma.

Ya bayyana cewa inganta rayuwar al'umma na taimakawa wajen ƙarfafa tsaro, tabbatar da zaman lafiya da kuma samar da yanayin da zai ba da damar samun ci gaba da wadata.

A nasa jawabin, Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa ta Gabas, Rear Admiral Okehie, wanda ɗan asalin yankin ne kuma ya taimaka wajen samar da ayyukan, ya nuna godiyarsa ga Babban Hafsan Sojin Ruwa bisa jagoranci da kuma ƙoƙarin tallafa wa ci gaban al'umma a sassa daban-daban na Najeriya.

Ya kuma nuna muhimmancin irin waɗannan ayyuka wajen inganta alaƙa tsakanin rundunar soji da fararen hula.

A nasu ɓangaren, mai martaba sarkin gargajiya da sauran shugabannin al'umma sun yi alƙawarin kula da kayayyakin da aka samar, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da su yadda ya kamata domin amfanin jama'a.

An gudanar da bikin cikin yanayi na farin ciki, inda aka kuma gabatar da kyaututtukan tunawa ga Babban Hafsan Sojin Ruwa, wanda ya wakilce shi, wanda ya taimaka wajen samar da ayyukan da sauran manyan baƙi.

Rahoto: Zainab Idris Bamalli

No comments