Breaking News

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Manomi Don Ya Mallake Gonarsa

Daga Shafi'i Haruna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta kama wani mutum mai shekaru 29, Godwin Yahaya, bisa zargin haɗa baki wajen sacewa da kashe wani manomi mai suna Jonah Isah a ƙauyen Zawudna, ƙaramar hukumar Munya ta jihar da nufin mallake gonarsa.

TNL HAUSA ta habarto cewa, ’yan sanda sun ce ana zargin Yahaya ya ɗauki hayar wani mutum ne mai suna Bashiru a shekarar 2024 domin ya sace Isah da nufin neman kuɗin fansa.

A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar ranar Asabar, an sace Isah ne a ranar 26 ga Yuni, 2026, bayan Bashiru da abokan burminsu sun kutsa gidan Isah da tsakar dare domin sace shi.

Rahotanni sun ce maharan sun kashe Isah tare da yin garkuwa da wasu iyalinsa da wasu mutane uku. An ce daga bisani masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 2.1 kafin su saki waɗanda suka yi garkuwa da su.

Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa waɗanda aka sace da waɗanda aka ceto kuma aka sako kwanan nan, sun ambaci sunan Yahaya, inda suka yi zargin cewa masu garkuwar sun bayyana musu shi ne ya ɗauke su haya domin gudanar da aikin.

Abiodun ya ce jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke yankin Kuchi sun kama Yahaya ne a ranar 27 ga Satumba, 2026, kafin daga bisani a miƙa shi ga ofishin ’yan sanda na Sarkin-Pawa domin gudanar da bincike.

A yayin yi masa tambayoyi, ana zargin Yahaya ya amsa cewa shi ne ya ɗauki Bashiru domin yin garkuwa da manomin, don su raba kuɗin fansar da za su samu. 

Mai magana da yawun ’yan sandan ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa Yahaya ya karɓe gonar marigayin bayan mutuwarsa, inda ya mayar da ita mallakinsa domin amfanin kansa.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike kan wanda ake zargin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha da ke Minna, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin. 

Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma tabbatar da gaskiyar zargin haɗa baki wajen satar mutanen da kisan manomin.

No comments