NYSC: Masu Garkuwa Sun Nemi Naira Miliyan 950 Kan ’Yan Bautar Ƙasa 19
Daga Hadi Bawa
Masu garkuwa da mutane sun nemi a biya su kuɗin fansa har Naira miliyan 950 domin sakin ’yan Najeriya 19 da suka tafi aikin bautar ƙasa (NYSC), waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar Imo.
’Yan bautar ƙasar na cikin fasinjojin motocin bas guda biyu da suka taso daga Ibadan, jihar Oyo, zuwa sansanonin horas da ’yan bautar ƙasa na jihohin Abia da Akwa Ibom, kafin ’yan bindiga su tare su a kan titin Owerri zuwa Onitsha, a Umunoha, jihar Imo, ranar Alhamis.
Manajan Daraktan kamfanin Uko Akwa Ibom Motors Nigeria Limited, Isiah Akpan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a, ya ce masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 50 kan kowane mutum.
Akpan ya ce motocin sun bar tashar Bodija/Samonda da ke Ibadan ranar Laraba, amma cunkoson ababen hawa a kusa da Benin, jihar Edo, ya jinkirta tafiyarsu. Daga bisani sun isa Onitsha da yamma, inda suka kwana a Oba saboda halin titin, kafin su ci gaba da tafiya da misalin ƙarfe 5 na safe ranar Alhamis.
Ya ce lokacin da motocin suka shiga jihar Imo, ’yan bindigar da suka fito daga daji suka tare su tare da kwashe fasinjoji 19, waɗanda duk ’yan bautar ƙasa ne, zuwa cikin daji. Direbobin sun samu damar tserewa, kuma suka sanar da jami’an tsaro da ke wani shingen bincike da ke kusa, lamarin da ya sa ’yan sanda da sojoji suka fara aikin neman waɗanda aka sace.
A ranar Alhamis da dare, rundunar ’yan sandan jihar Imo ta ce an ceto mutane 10, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da neman sauran waɗanda aka sace.
Sai dai kakakin rundunar, Henry Okoye, ya ce ba zai iya tabbatar da cewa waɗanda aka ceto suna cikin ’yan bautar ƙasar da aka sace ba.
Wasu iyalan waɗanda aka sace sun ce masu garkuwar sun tuntuɓe su ta wayoyin ’ya’yansu, tare da neman Naira miliyan 50 kan kowane mutum, lamarin da ya ƙara jefa iyalan cikin fargaba.


No comments