Kasashe Masu Tasowa Na Fuskantar Matsin Bashi i– IMF da Bankin Duniya
Daga Journalist Hauwa'u Maikudi
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya sun bayyana damuwa kan yadda ƙasashen Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa ke fuskantar ƙarin nauyin bashi da ƙarancin damar samun ayyukan yi.
Hukumomin sun bayyana waɗannan ƙalubale ne yayin taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya da aka gudanar a birnin Bangkok na ƙasar Thailand.
A cewar rahotannin, yawan kuɗin da ƙasashe ke kashewa wajen biyan basussuka na rage kuɗaɗen da gwamnatoci za su iya warewa domin ayyukan raya ƙasa, ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.
Haka kuma, tsadar rance, sauye-sauyen tattalin arzikin duniya da raguwar tallafin ƙasashen waje na ƙara matsin tattalin arziki ga ƙasashe masu tasowa.
A wani rahoto da ya shafi taron, Ministan Kuɗi na Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ƙasashe masu tasowa na biyan kusan dala biliyan 500 fiye da ƙasashe masu ci gaba ta fuskar kuɗin hidimar bashi.
Ya kuma yi kira da a sake fasalin tsarin cibiyoyin hada-hadar kuɗi na duniya domin inganta damar ƙasashe masu tasowa wajen samun tallafin kuɗi da sauƙaƙa musu nauyin bashi.
Masana na ganin cewa zuba jari a samar da ayyukan yi, inganta ilimi da ƙwarewar matasa, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida na da muhimmanci wajen rage waɗannan matsaloli.


No comments