Breaking News

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Warware Matsalar Da Ke Ci Wa Ma'aikatan Gwamnati Tuwo A Ƙwarya

Daga Hadi Bawa 

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen matsalolin da ake samu na tsaiko wajen yi wa ma’aikata ƙarin girma a hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatarsa, tare da amincewa da biyan tsoffin kwanturololi janar da mataimakansu na hukumar shige da fice albashi har ƙarshen rayuwarsu.

TNL HAUSA ta jiwo cewa, Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin bikin rufe horo kan tsarin kula da iyakoki da gudanar da harkokin shige da fice na musamman (BCIMS), wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar shige da fice da ke Abuja.

Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ɗaukar matakan magance tsaikon ɗaukaka matsayin ma’aikata, inda ya bayyana cewa aƙalla ma’aikata 50,000 ne suka samu ƙarin girma da sabbin muƙamai cikin shekaru uku.

Ya ce: “Wannan abu bai taɓa faruwa a baya ba, amma Tinubu ya yi hakan. Haka kuma, ya ƙara yawan ɗaukar sabbin ma’aikata, inda yanzu aka samu sabbin ma’aikata aƙalla 40,000 a lokaci guda.

“Dangane da ƙarin albashi kuwa, Shugaban ƙasa ya yi hakan. Haka ma game da alawus na haɗari da na musamman.”

Tunji-Ojo ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda yake kula da jin daɗin ma’aikatan da ke bakin aiki da waɗanda suka yi ritaya, musamman dangane da ƙarin kuɗaɗen fansho ga tsoffin shugabannin hukumar shige da fice.

Ya ce a baya, tsoffin kwanturololi janar na hukumar suna karɓar fansho na kusan naira 130,000, wanda a cewarsa, bai wadatar ba.

“Amma me Shugaban ƙasa ya yi? Ya sanya hannu tare da amincewa da biyan kwanturololi janar da mataimakansu albashi har ƙarshen rayuwarsu.

“Shugaban ƙasa ya kula da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar fiye da kowane shugaban ƙasa a tarihin Najeriya. Ya ba ku duk abin da yake da shi.

“Abin da yake nema daga gare mu a matsayin ma’aikatan gwamnati kawai shi ne mu gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, domin faranta ran ’yan Najeriya. Duk abin da muka nema daga gare shi, ya yi mana. Wannan shi ne mafi ƙarancin abin da za mu iya yi domin rama alherinsa,” in ji shi.

Ministan ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai hangen nesa, yana mai cewa manufofinsa an tsara su ne domin samar da sakamako mai ɗorewa wanda zai amfani ƙasar nan na dogon lokaci.

Tunji-Ojo ya ce a ƙarƙashin shirin Renewed Hope, Shugaba Tinubu yana gina tsarin da zai dawwama, kuma ya ci gaba da aiki yadda ya kamata ko bayan ya bar mulki.

Ya ce Shugaban ƙasar yana mai da hankali ne kan makomar Najeriya maimakon abin da za a samu nan take.

“Shugaba Bola Tinubu bai mayar da hankali kan abin da za a samu a yanzu kawai ba, sai dai makomar ƙasa. Ya fahimci cewa ƙasashe masu arziki ba sa cinye irin da za su shuka, a maimakon haka, suna shuka shi ne domin samun yalwa a nan gaba.

“Abin da wannan Shugaban ƙasa yake yi shi ne shuka irin da zai samar da yalwa a nan gaba,” in ji ministan.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya fahimci cewa ba zai ci gaba da riƙe muƙamin shugaban ƙasa har abada ba, amma hukumomin gwamnati za su ci gaba da wanzuwa. Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne irin tsarin da za a bari domin amfanin al’umma masu zuwa.

Waɗannan matsalolin dai sun jima suna ci wa ma'aikata tuwo a ƙwarya.

No comments