Breaking News

DSS Ta Kama Ɗan Tsohon Shugaban Hukumar Gyaran Fansho Ta Ƙasa.

Daga Journalist Hauwa'u Maikudi

Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta kama Faisal Abdulrasheed Maina, ɗan tsohon shugaban hukumar gyaran fansho ta ƙasa, Abdulrasheed Maina, tare da miƙa shi ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun ce jami’an DSS sun kama Faisal ne a yankin Karsana da ke Abuja, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya dawo Najeriya a ɓoye.

Faisal ya kasance yana fuskantar shari’ar zargin karkatar da kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya, bayan da aka gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2020.

A watan Oktoban 2021, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 a gidan yari. Sai dai a watan Nuwamban 2022, kotun ɗaukaka ƙara ta rage hukuncin zuwa shekara bakwai, tare da tabbatar da hukuncin da aka yanke masa.

Miƙa Faisal ga EFCC na da alaƙa da matakan da ake sa ran hukumar za ta ɗauka kan hukuncin da kotu ta yanke masa.

No comments