Diri Ya Yi Watsi da Sukar Duke Kan Babbar Hanyar Lagos-Calabar
By Zainab Idris Bamalli
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yi watsi da sukar da tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, ya yi kan aikin gina babbar hanyar Lagos-Calabar, yana mai cewa ana iya aiwatar da aikin duk da kasancewar yankin dausayi.
Duke ya bayyana aikin a matsayin wanda zai yi wahalar yiwuwa saboda yanayin ƙasar mai fadama, inda ya ce za a buƙaci gina daruruwan gadoji.
Sai dai Gwamna Diri ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar gina manyan hanyoyi da gadoji a yankunan da ke da irin wannan yanayi, ciki har da hanyoyin Nembe-Brass da Sagbama-Ekeremor-Agge, da kuma gadar da ta ratsa Kogin Nun.
Ya ƙara da cewa babbar hanyar mai tsawon kilomita 750, wadda za ta ratsa jihohin bakin teku tara, na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga a yankunan da ke da wahalar isa.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa aikin yana da muhimmanci ga al’ummar Ijaw, yana mai cewa ya kasance cikin buÆ™atun da Æ™ungiyar Ijaw National Congress ta daÉ—e tana gabatarwa ga gwamnatocin tarayya.
Diri ya yi gargaÉ—in cewa bai kamata a mayar da ayyukan ci gaba siyasa ba, musamman a lokacin zaÉ“e, domin hakan na iya cutar da al’ummar da ake neman Æ™uri’unsu.


No comments