Breaking News

IMF Ta Shawarci Nijeriya Kan Tallafin Man Fetur

By Zainab Idris Bamalli

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya da kada ta dawo da tallafin man fetur, inda ya buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen tallafa wa marasa ƙarfi domin rage tasirin hauhawar farashin makamashi.

IMF ta bayyana cewa tallafin man fetur na bai ɗaya yana kashe kuɗaɗe masu yawa, kuma masu matsakaicin ƙarfi da masu kuɗi ne suka fi amfana da shi.

Daraktan sashen kasafin kuɗi na IMF, Rodrigo Valdés, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026 da ake gudanarwa a Bangkok, Thailand.

No comments