AN HORAR DA MATA SAMA DA 100 A KADUNA KAN SANIN HAKKOKINSU
Daga Zainab Idris Bamalli
Wata shugabar ƙungiyar sa-kai, Hajiya Jamila Lawal, ta horar da mata sama da 100 a unguwar Rigasa da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, kan sanin hakkokin mata, hanyoyin magance rikicin cikin gida da kuma sasanta rikice-rikice a cikin al'umma.
Hajiya Jamila, wadda ita ce shugabar ƙungiyar Rigasa Yau-da-Gobe Association, ta fara gudanar da horon ne domin yaɗa ilimin da ta samu a wani taron horaswa kan ayyukan taimakon shari'a, wanda ofishin jakadancin Jamus da ke Abuja ya shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Sasanta Rikice-rikice ta Addinai, wato Interfaith Mediation Centre (IMC), da ke Kaduna.
Shirin na da nufin ƙarfafa wa mata gwiwa tare da ba su ilimin da zai taimaka musu wajen fahimtar hakkokinsu, magance matsalolin cin zarafi a cikin gida da kuma taimakawa wajen warware saɓani a tsakanin iyalai da al'umma.
Hajiya Jamila Lawal ta bayyana cewa ya zama wajibi a yaɗa ilimin da aka samu, duba da muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen magance matsalolin iyali, cin zarafi da sauran ƙalubalen zamantakewa.
Ta ce bai wa mata ilimin hakkokinsu da hanyoyin samun taimako zai ba su damar fuskantar matsalolin da suka shafi rayuwarsu da ta iyalansu hb cikin basira.
A nata ɓangaren, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, Maryam Mohammed, ta bayyana farin cikinta bisa damar da aka ba ta na koyon abubuwan da suka shafi hakkokin mata, tana mai cewa wannan ne karon farko da ta samu irin wannan ilimi.
Maryam ta kuma yi alƙawarin yaɗa ilimin ga sauran mata da ke maƙwabtaka da al'ummarsu, domin tabbatar da cewa mutane da dama sun amfana da shirin.
Shi ma mataimakin daraktan Cibiyar Sasanta Rikice-rikice ta Addinai, wato Interfaith Mediation Centre, Mista Samson Auta, ya bayyana gamsuwarsa da yadda matan suka karɓi shirin, musamman yadda suka nuna sha'awar mayar da ilimin zuwa cikin al'ummominsu domin horas da wasu.
Mista Auta ya ce tun bayan fara aiwatar da shirin a jihar Kaduna, an samu ɗaruruwan mata da suka amfana da ilimi da ƙwarewa kan sanin hakkokinsu, magance cin zarafi a cikin gida, sasanta rikice-rikice da kuma taimaka wa sauran mata.
Ya ƙara da cewa shirin na nuna yadda mata za su iya taka rawa wajen wayar da kan al'umma, inganta samun taimakon shari'a, hana cin zarafi da kuma ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna.
Masu shirya shirin na fatan cewa ci gaba da gudanar da irin wannan horo zai faɗaɗa yawan matan da za su amfana da ilimin, tare da samar da ƙwararrun mata a cikin al'ummomi waɗanda za su taimaka wajen wayar da kai, gano matsaloli tun da wuri da kuma tura waɗanda abin ya shafa zuwa hukumomi da cibiyoyin da suka dace domin samun taimako.
Daga Zainab Idris Bamalli, Kaduna.


No comments