Breaking News

PDP TA NUNA DAMUWA KAN CIRE SUNAYEN WASU ’YAN TAKARART DA INEC TA FITAR


Daga Zainab Idris Bamalli

Jam’iyyar PDP ta bayyana damuwarta kan rashin sanya sunayen wasu daga cikin ’yan takararta a jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta fitar.

Jam’iyyar ta ce tuni ta fara tattaunawa da hukumar domin ganin an warware matsalar ta hanyar lumana, bisa tanadin doka da ƙa’idojin gudanar da zaɓe.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Jungudo Haruna Mohammed, ya fitar, PDP ta tabbatar da cewa tana ɗaukar lamarin da muhimmancin da ya dace, tare da neman mafita cikin lumana.

Sanarwar ta kuma buƙaci ’yan takarar da abin ya shafa, mambobin jam’iyyar da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu tare da yin haƙuri yayin da tattaunawar da INEC ke ci gaba.

Rahotanni sun nuna cewa jerin sunayen da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ya ƙunshi ’yan takara 13 a jihar Ogun da kuma 16 a jihar Gombe, ba tare da sunan wani ɗan takarar PDP a jihohin biyu ba.

Daga cikin fitattun ’yan takarar da ba a ga sunayensu a jerin ba akwai Ladi Adebutu a jihar Ogun da kuma Isa Ali Pantami a jihar Gombe.

Jam’iyyar PDP na fatan tattaunawar da take yi da INEC za ta taimaka wajen warware matsalar, tare da tabbatar da bin dokoki da ƙa’idojin zaɓe yayin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

No comments