Breaking News

Amnesty International Ta Yi Allah-Wadai Da Kamawa Da Tsare 'Yar Jarida A Kaduna

Daga Hadi Bawa 

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kama ’yar jarida mai shekaru 23, Farida Isiak, tare da gaggawar yanke mata hukuncin ɗaurin shekara huɗu a Kotun Shari'ar, ko kuma biyan tarar sama da Naira miliyan ɗaya saboda wallafa rubutu a Facebook.

Ƙungiyar ta bayyana cewa matakan da aka ɗauka a kanta sun samo asali ne daga ƙoƙarinta na fallasa cin zarafin da ’yan sanda ke yi wa iyayenta da suka kama suka tsare saboda saɓani da maƙwabtaka da suka samu a kan Naira 100. 

Ta ce yanke mata hukuncin ɗaurin shekara huɗu bayan shari’ar da ta kira ta bogi da tauye mata haƙƙi, hakan ya saɓa wa dokokin Nijeriya.

TNL HAUSA ta samu rahoton cewa, Farida Isiak, wadda take aiki a gidan rediyon Nagarta da ke Marabar Jos, Kaduna, ta shiga hannun ’yan sanda ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren Litinin, 20 ga Oktoba, 2026. 

DPO da ke kula da ofishin ’yan sanda na Mararaban Jos, Usman Adamu ne ya jagoranci kama 'yar jaridar sakamakon ƙaramin saɓani da aka samu tsakanin mahaifiyarta da wata maƙwabciya kan canjin kuɗin Naira 100 na ciniki gawayi.

A cewar Amnesty International, ’yan sanda sun fara kama mahaifiyar Farida, daga bisani kuma suka tsare mahaifinta lokacin da ya je neman jin bahasin kama matarsa. 

Ƙungiyar ta ce jami’an sun yi amfani da tsare iyayen nata a matsayin hanyar tilasta wa Farida zuwa ofishin ’yan sanda.

Bayan isowarta ofishin, jami’an ’yan sanda sun zarge ta da ɓata musu suna sakamakon wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta soki yadda suka yi wa iyayenta abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da saɓa doka. 

Duk da cewa Farida ta bi umarnin ’yan sandan na goge saƙon tare da ba da haƙuri, da fatan hakan zai taimaka wajen sakin iyayenta, jami’an sun ci gaba da tsare ta, sannan suka gurfanar da ita cikin gaggawa a gaban kotun Shari’a da ke Kawo.

Ƙungiyar ta ce Alƙalin kotun ya yanke wa Farida hukuncin ɗaurin shekara huɗu a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira miliyan 1.75 bisa zargin ɓata suna. 

Amnesty International ta soki yadda kotun ta yi watsi da zargin rashin bin doka da jami’an ’yan sanda suka yi tun farko, da kuma matakan da suka jawo faruwar lamarin.

Amnesty International ta bayyana kama Farida, tsare ta da kuma gaggawar yanke mata hukunci a matsayin cin zarafin iko da ’yan sanda suke da shi, tare da amfani da tsarin shari’a wajen danne ’yancin faɗin albarkacin baki da tsoratar da ’yan jarida. 

Ta ce amfani da tsare iyayen mutum domin tilasta masa miƙa kansa ga ’yan sanda ya saɓa wa ƙa’idojin doka, yayin da neman a ɗora wa jami’an gwamnati alhakin ayyukansu haƙƙi ne da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci rundunar ’yan sandan jihar Kaduna da hukumomin shari’a na Najeriya su gaggauta sakin Farida Isiak, su janye dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata, tare da soke tarar da aka yanke mata. 

Haka kuma, ta yi kira ga rundunar ’yan sandan Najeriya da ta gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yadda jami’an da abin ya shafa suka tsare iyayen Farida. 

Amnesty International ta kuma buƙaci hukumomin Najeriya su daina amfani da tuhumar ɓata suna da tsarin shari’a wajen musguna wa ’yan jarida ko takura wa ’yancin faɗin albarkacin baki.

No comments