Breaking News

NERC Ta Shiga Tsakani, An Dawo Da Wutar Lantarki A Gidan Wani Mazaunin Bauchi Bayan Kwanaki 26 Da katse Ta


Daga Hauwa'u Maikudi TNL HAUSA 

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta shiga tsakani, inda aka dawo da wutar lantarki a gidan ɗan jarida Nasiru Hassan da ke Yalwan Makaranta a jihar Bauchi, bayan shafe kwanaki 26 a katse.

An katse wutar gidan Hassan a ranar 23 ga Satumba, 2026, bayan samun saɓani tsakanin sa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JED) kan rukunin kuɗin wutar da ya dace da gidan.

Hassan ya ce tun da farko JED ta tantance gidan nasa, ta sanya masa mitar biya kafin amfani da wuta, kuma ya sayi units kafin a katse wutar.

Sai dai, a cewarsa, wata tawagar sa-ido ta JED ta dage cewa gidan yana cikin rukuni na A, kafin ta katse wutar ba tare da sanarwar rubutacciya ba.

Bayan katsewar, Hassan ya ce ya shigar da ƙorafi a ofishin JED da ke Bauchi a ranar 23 ga Satumba, amma ba a dawo da wutar ba, lamarin da ya sa ya kai ƙorafinsa ga NERC a ranar 16 ga Oktoba, 2026.

Ya ce bayan shiga tsakani da hukumar ta yi, an dawo da wutar lantarki a gidansa a yammacin ranar 19 ga Oktoba, 2026.

Duk da dawo da wutar, Hassan ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da neman haƙƙinsa, inda ya ce yana shirin ɗaukar matakin shari’a kan JED bisa katsewar wutar da ya ce ta faru ba tare da sanarwar rubutacciya ba.

Ya kuma yi kira da a wayar da kan al’umma game da haƙƙoƙin masu amfani da wutar lantarki da kuma hanyoyin kai ƙorafi ga NERC idan aka samu saɓani da kamfanonin rarraba wuta.

Lamarin ya sake jawo hankali kan muhimmancin bayyana wa masu amfani da wuta dalilan katse musu lantarki, tare da samar da ingantattun hanyoyin warware saɓani kan rarraba masu kuɗin wuta, da kuma samar da hanyoyin warware Sabani cikin Gaskiya da Adalci.

No comments