Breaking News

ZAMFARA: INEC Ta Ci Gaba Da Raba KatinPVC A Ofisoshin Kananan Hukumomi 14 Dake Fadin Jihar

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Jihar Zamfara ta sanar da kammala raba katin zaɓe na dindindin (PVC) a matakin unguwanni, tare da umartar masu zaɓe da ba su karɓi katunansu ba da su je ofisoshin hukumar da ke ƙananan hukumomi 14 na jihar domin karɓa.

Kwamishinan Zaɓe na jihar, Dr. Mahmuda Isah, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen zaɓen 2027 da aka gudanar a Gusau ranar Laraba.

Ya ce an kammala raba katunan a matakin unguwanni ranar 15 ga Oktoba, 2026, yana mai jaddada cewa karɓar katin PVC kyauta ne, kuma dole ne kowane mai zaɓe ya karɓi nasa da kansa.

Kwamishinan ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin farar hula su ƙara wayar da kan jama'a kan muhimmancin karɓar katunan.

A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ahmad Bello, ya ce za a mayar da rumfunan zaɓen da ba a iya isa gare su saboda matsalolin tsaro zuwa wuraren da suka fi aminci.

Ya tabbatar da cewa ’yan sanda za su yi aiki tare da INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓen 2027 cikin kwanciyar hankali.

Shi ma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed, ya yi alƙawarin ci gaba da wayar da kan al'ummarsa kan karɓar PVC da sauran harkokin zaɓe.

Sai dai jam'iyyun siyasa sun nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan jihar, tare da kira ga INEC da hukumomin tsaro da su inganta shirye-shiryensu.

Fassara: Zainab Idris Bamalli

No comments