Za A Bai Wa Magatakardan BUK Lambar Yabo Ta AfricanAGE Ta 2026
Daga Shafi'i Haruna
An zaɓi Magatakardar Jami’ar Bayero, Kano (BUK), Malam Haruna Aliyu, domin karɓar lambar yabo ta AfricanAGE Academic Excellence and Educational Leadership Award ta shekarar 2026, saboda gudunmawar da ya bayar wajen jagoranci a fannin ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire, bincike da bunƙasa Jami’a.
TNL HAUSA ta samu rahoton cewa wannan bayanin na ƙunshe ne cikin wata wasiƙar mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2026, wadda Kwamitin Amintattu na AfricanAGE da Hukumar Editocin Mujallar AfricanAGE International Magazine suka aika, bayan gudanar da wani cikakken tsarin tantancewa da zaɓe.
A cewar wasiƙar, an gano cewa Haruna Aliyu na cikin shugabannin da suka fi tasiri a ɓangaren ilimi a Najeriya, bayan wani bincike da tantancewa mai zaman kansa da hukumar editocin mujallar ta gudanar a watan Agusta na 2026.
An ce tantancewar ta duba jagoranci a fannin ilimi, ingancin karatu, yawan bincike, ƙirƙire-ƙirƙire, gudanarwa, bunƙasar Jami’a, iya hulɗa da jama'a da kuma gudunmawar da aka bayar wajen ci gaban ilimi.
Kwamitin ya bayyana cewa Mujallar na karrama mutanen da jagorancinsu, amincinsu, ƙirƙire-ƙirƙirensu da jajircewarsu suka taimaka wajen inganta ilimi, bincike, bunƙasa ƙwarewar ɗan Adam da samar da ingantaccen ilimi a Afirka.
Wasíƙar ta ƙara da cewa jajircewar Aliyu wajen bunƙasa Jami’ar Bayero da ke Kano, ilimi, jagoranci da gudanar da harkokin ilimi ne ya ba shi matsayin wanda ya cancanci karramawar.
An tsara gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, a International Conference Centre (ICC), Abuja, inda za a bai wa waɗanda aka karrama da lambar yabo da takardar shaidar ƙwarewa, a gaban manyan baƙi daga jami’o’i, jami'an gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin ƙwararru da ’yan kasuwa.
Wasiƙar ta ce tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Farfesa Jerry Gana ne zai jagoranci taron, yayin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata David Mark, zai kasance Babban Baƙo. Ana kuma sa ran Mai Martaba Sarkin Nupe, Alhaji (Dr.) Yahaya Abubakar, zai kasance uban taron.
Wasiƙar dai na ɗauke ne da samu hannun Yarima Sado A. O. Patrick, Shugaban Kwamitin Amintattu na AfricanAGE Awards of Excellence 2026 da Uwargida Philomina Onoshovhena, Daraktar Zartarwa ta AfricanAGE Nigeria Limited.


No comments