Breaking News

An Kammala Tantance Ma’aikata 546 Da Aka Mayar Da Su Dindindin A Kano

Daga Hadi Bawa 

Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar Kano ta kammala tantance ma’aikata 546 da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da mayar da su cikakkun ma’aikatan gwamnati na dindindin.

Shugabar hukumar, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, ce ta jagoranci aikin tantancewar, wanda aka gudanar domin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikatan da kuma cika sharuɗɗan mayar da su ma’aikatan dindindin.

A yayin tantancewar, shugabar ta ja hankalin ma’aikatan da su kasance masu gaskiya, riƙon amana da bin ƙa’idojin aikin gwamnati, domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Hajiya Garko ta kuma buƙace su da su ɗauki sabon matsayin da suka samu a matsayin wata dama ta ƙara jajircewa wajen yi wa al’umma hidima da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Bayan kammala tantancewar, an tura ma’aikatan zuwa ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban, bisa la’akari da ilimi, kwarewarsu da buƙatun aikin gwamnati.

Sabbin ma’aikatan sun nuna godiyarsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan amincewa da mayar da su ma’aikatan dindindin, tare da bayyana cewa matakin ya ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Sun kuma yi alƙawarin yin aiki tuƙuru, da gaskiya da riƙon amana, domin bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ayyukan gwamnati da ci gaban jihar Kano.

No comments