Breaking News

Me Ya Jawo Mutuwar Matasa 37 Da Ke Tsare A Hannun NSCDC A Neja?

Daga Hadi Bawa

Aƙalla matasa 37 da ake zargi da laifin gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne suka mutu yayin da suke tsare a hannun Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) a jihar Neja, lamarin da ya jawo cece-kuce da kuma fara bincike daga hukumomin tsaro. 

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tabbatar da mutuwar mutanen, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ba za a bar shi ya wuce haka kawai ba.

TNL HAUSA ta gano cewa, matasan da suka rasu na daga cikin waɗanda jami’an NSCDC suka kama a ranakun 15 da 16 ga Satumba, yayin wani samame da aka gudanar a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar, domin daƙile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ta ce samamen ya kai ga kama mutane da dama tare da ƙwato wasu kayayyaki daga wuraren da aka gudanar da aikin.

Kwamandan NSCDC na jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, wanda lamarin ya faru a lokacin da yake jagorantar rundunar jihar, ya bayyana cewa an gano gawawwakin mutanen da safiyar 17 ga Satumba. 

A bayanin farko da rundunar ta bayar, an danganta mutuwar da abin da aka bayyana a matsayin zargin ɓarkewar wata cuta, sai dai hedikwatar NSCDC ta ƙasa ta ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar ba, kuma sai an kammala binciken likitoci da na ɗakunan gwaje-gwaje kafin a tabbatar da dalilin.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa mutuwar ta jawo zargin wasu daga cikin al’ummar yankin da ke ganin akwai wasu dalilai da ka iya haddasa mutuwar, ciki har da yanayin wurin da aka tsare waɗanda aka kama. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da waɗannan zarge-zargen a hukumance ba, yayin da ake jiran sakamakon binciken lafiya da na hukumomin tsaro.
Gwamnatin jihar ta kuma ce za a gudanar da binciken gawawwakin tare da yin 'autopsy' domin gano ainihin abin da ya faru.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Neja, Adamu Abdullahi Elleman, ya bayar da umarnin fara bincike kan lamarin, inda ya umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan da ke kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar, SCID, da ke Minna, da ya jagoranci binciken domin gano abubuwan da suka kai ga mutuwar waɗanda ake tsare da su.

Rundunar ’yan sandan ta kuma yi kira ga iyalan mamatan da sauran jama’a da ke da muhimman bayanai kan lamarin da su gabatar da su ga masu binciken.

Haka kuma, Gwamna Umaru Bago ya sanar da kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin mutuwar matasan da kuma tabbatar da abin da ya faru a wurin da aka tsare su. 

Kwamitin yana ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Yakubu Garba, yayin da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Maurice Magaji, ke matsayin sakatare. 

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a gudanar da binciken ƙwaƙƙwaran masana da gwaje-gwajen gawarwakin domin gano ainihin musabbabin mutuwar.

A halin da ake ciki, an dakatar da Kwamandan NSCDC na jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye da sauran jamiansa, domin bai wa binciken damar gudana ba tare da tsangwama ba. 

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya, ta hannun Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ta bayar da umarnin dakatar da kwamandan tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin. 

Haka kuma, NSCDC ta ƙasa ta kafa tawaga ta musamman domin binciken yanayin lafiyar waɗanda aka kama tun kafin tsare su, lokacin da ɗauka a tsare a hannun rundunar, yanayin wurin tsarewar da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su.

No comments