Yadda Aka Yi Garkuwa Da Mijina, Aka Kashe Shi -Matar Dakta Sadiq ABU
Daga Hadi Bawa
An kashe wani Malami a Sashen Kwalejojin Koyon Aikin Noma na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dakta Iliyasu Abubakar Sadiq, bayan wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a gidansa da ke unguwar Tudun Muntsira a Samaru Zariya.
TNL HAUSA ta jiwo matar marigayin, Hajiya Baraka, tana cewa lamarin ya faru ne da misalin Ęarfe 10 na safiyar Lahadi, 20 ga Satumba, 2027.
Ta ce suna gonar ne lokacin da karen gidansu ya fara haushi, lamarin da ya sa mijinta ya fito domin duba abin da ke faruwa, amma jim kaÉan sai ya dawo yana cewa: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
Baraka ta ce mijinta ya umarce ta da su taimaka wajen rufe Ęofar gidan, amma yayin da suke ĘoĘarin rufe ta, ‘yan bindigar suka tura Ęofar daga waje suna barazanar kashe su idan ba su buÉe ba.
A cewarta, maharan huÉu ne Éauke da makamai, kuma sun fasa wani Éangare na Ęofar kafin su shiga gidan da Ęarfi.
Ta ce mijinta ya yi ĘoĘarin tserewa, amma suka tare shi, suna cewa ko ya gudu, iyalinsa za su ci gaba da kasancewa a wurin.
Matar ta ce ‘yan bindigar ba su rufe fuskokinsu ba, inda biyu daga cikinsu suka riĘe mijinta, yayin da sauran suka tambaye ta kuÉi da inda suke ajiye kayayyaki masu daraja.
Barka ta ce ta bayyana musu cewa ba su da kuÉi, kuma ba su ne mamallakan gonar ba, domin sun zo ne kawai domin gudanar da ayyukansu.
Bayan da suka zarge ta da Ęarya, Éaya daga cikin maharan ya yi mata barazanar kashe ta, sannan ya mare ta tare da umartar yaransu da ke kuka da su yi shiru.
Baraka ta ce ta kwantar da hankalin yaran tare da gaya musu su yi addu’a, tana mai cewa su Musulmai ne, kuma addu’a ce makaminsu.
Daga nan maharan suka nemi wayar mijinta da katin ATM. Bayan sun fahimci cewa ba za su samu kuÉi ba, sai suka sanar da cewa za su tafi da Dakta Sadiq.
Ta ce ita da mijinta sun roĘe su da su bar shi, suna tunasar da su cewa suna da Ęananan yara da suke dogaro da shi, amma roĘon bai sa sun sauya ra’ayi ba.
A cewar Baraka, ‘yan bindigar sun ja Dakta Sadiq suka tafi da shi, yayin da ita kuma ta gudu zuwa wani gida da ke kusa domin neman taimako.
Ta sanar da mutanen yankin, inda wasu daga cikin mazauna garin suka bi sawun maharan zuwa daji, amma ba su same su ba.
Bayan wasu sa’o’i, an sanar da ita cewa an gano gawar mijinta a kusa da Ęauyen Karau-Karau, inda aka ce an harbe shi a ka, sannan maharan suka kwashe kayayyakin da ke jikinsa suka bar gawarsa a wurin.
An yi garkuwa da mijina, aka kashe shi — matar malamin ABU
An kashe wani malami a Sashen Kwalejojin Noma na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dakta Iliyasu Abubakar Sadiq, bayan wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi daga gonarsa da ke Tudun Muntsira, bayan harabar Samaru ta jami’ar.
Haifaffen jihar Jigawa, Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya tara.
Dakta Sadiq malami ne kuma mai bincike a Sashen Kwalejojin Aikin Gona na ABU, tare da koyar da darussan da suka shafi ilimin Ęwari da aikin gona.
Shugaban Sashen Kwalejojin Aikin Gona na ABU, Farfesa Bashir Ahmed Babaji, ya bayyana rasuwar Dakta Sadiq a matsayin babban rashi ga Jami’ar, yana mai cewa marigayin mutum ne mai Ęwazo da sadaukar da kai.
Duk ĘoĘarin da Wakilinmu ya yi domin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ko kuma hukumomin Jami'ar ABU, haĘarsa ba ta cimma ruwa ba.


No comments