Iyalan Masu Haƙar Ma’adinai Da Suka Rasu A Hannun NSCDC A Neja Sun Nemi Adalci
Daga Hadi Bawa
Iyalan mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne, waɗanda suka rasu bayan da jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) suka kama su a jihar Neja, sun nemi a yi musu adalci tare da biyan su diyya.
Iyalai da dama da suka rasa ’yan'uwansu sun shaida wa jaridar PUNCH cewa, an hana su ganawa da iyalan nasu, daga bisani aka sanar da su cewa sun rai ya yi halinsa.
Sun ce a lokuta da dama idan suka je ofishin NSCDC domin ganin waɗanda aka tsare ko kai musu abinci, jami’an kan ce masu su sake dawowa. Sai daga baya suka samu labarin cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama sun rasu.
Wasu daga cikin ’yan uwan mamatan sun kuma yi zargin cewa an bar gawawwakin na tsawon sa’o’i kafin a sauke su daga cikin motar asibiti a Babban Asibitin Minna. Sun ce wasu daga cikin gawawwakin matasan na da kumfa da jini a bakinsu.
TNL Hausa ta gano cewa waɗannan zarge-zargen sun sake haifar da tambayoyi kan abin da ya faru da masu hakar ma’adinai daga lokacin da aka kama su har zuwa rasuwarsu, da kuma yanayin da ake tsare su, ko sun samu kulawar da ta dace, da kuma ainihin abin da ya haddasa mutuwarsu.
Musa Aliyu mai shekara 63, ya shaida wa PUNCH cewa lamarin ya ƙara jefa iyalinsa cikin mawuyacin hali bayan rasuwar ’ya’yansa biyu, Ibrahim mai shekara 17 da Abubakar mai shekara 12.
Aliyu, wanda ya ce ya kwashe sama da watanni 14 yana kwance saboda rashin lafiya, ya ce ’ya’yansa ne ke taimaka masa wajen sayen magunguna da kuɗin da suke samu daga aikin haƙar ma’adinai kafin su rasa rayukansu a can.
Ya ce: “’Ya’yana sun bar gida zuwa wurin haƙar ma’adinai kamar yadda suka saba domin neman abin da za su samu. Su ne suke sayo min magani tun lokacin da na fara rashin lafiya. Amma wannan karon ba su dawo ba.
“Matata ta je neman su, sai aka gaya mana cewa jami’an NSCDC sun kama su. Da muka je wurin, ba mu samu damar ganinsu ba. Daga baya aka sanar da mu cewa sun mutu.
“Mun gane gawawwakin su a Babban Asibitin Minna. Ba mu da ikon yin faɗa da hukumomi. Mun bar komai ga Allah.”
Wani mahaifi da ya rasa ɗansa, Lawal Muhammed, ya ce ya rasa ɗansa mai shekara 15, Suleiman, bayan da jami’an suka hana shi da sauran iyaye ganin ’ya’yansu bayan kama su.
Muhammed ya ce lokacin da ya dawo gida ranar Laraba, matarsa ta sanar da shi cewa jami’an NSCDC sun kama ɗansa a wurin haƙar ma’adinai. Daga nan ya tafi ofishin NSCDC tare da ɗan’uwansa da wasu iyayen yaran a daren.
Ya ce jami’an sun umarce su da su dawo washegari.
A cewarsa, da suka koma da safe ɗauke da abinci domin kai wa waɗanda aka tsare, sai aka sanar da su cewa ɗansa ya rasu.
“Na kasance a ofishin NSCDC lokacin da ake loda gawawwakin cikin motar asibiti, kuma na bi su zuwa Babban Asibitin Minna. Ba su sauke gawawwakin daga cikin motar ba sai wajen ƙarfe 6 na yamma,” in ji shi.
Muhammed ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wani jami’in da aka samu da hannu a lamarin.
“Ina adalcin da muke ta nema? Ina son gwamnati ta gurfanar da jami’an da ke da hannu a wannan lamari domin hakan ya zama darasi ga wasu. Jami’ai ne waɗanda suka rantse za su kare mutane,” in ji shi.
Muhammad Musa, wanda ya rasa ɗan’uwansa Abubakar mai shekara 17, ya kuma yi zargin cewa an hana ’yan'uwan waɗanda aka kama shiga ofishin NSCDC lokacin da suka je neman bayanai ranar Alhamis.
Wani mahaifi da ya rasa ɗansa, Mohammad Nuru, ya shaida wa PUNCH cewa ya rasa ɗansa Sabiu, da kuma wasu ’yan'uwa da maƙwabta tara a lamarin.
Ya ce an hana shi ganin waɗanda aka tsare lokacin da ya kai musu abinci ofishin NSCDC bayan kama su.
Nuru ya ce da dama daga cikin waɗanda aka kama matasa ne, ciki har da ’yan shekara 14 da 15, waɗanda suka koma aikin haƙar ma’adinai domin taimaka wa iyalansu.
Shi ma wani mahaifi mai suna Mohammed Mankuɗi ya ce ya samu labarin mutuwar mutanen ne ta hanyar saƙonnin da ke yaɗuwa a Facebook.
Hakan ya zo ne yayin da kwamitin bincike mai zaman kansa da gwamnatin tarayya ta kafa domin binciken lamarin ya fara zaman bincikensa ranar Laraba.
Tawagar likitocin kwamitin ta fara aiki gadan-gadan domin gano musabbabin mutuwar, yadda ta faru da kuma yanayin da ta auku.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya kafa kwamitin ranar Talata. Tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Jonathan Kure, ne ke jagorantar kwamitin, yayin da Farfesa Isa Hayatu Chiroma, SAN, yake matsayin sakatare.
Kwamitin ya fara zaman bincikensa ranar Laraba, kamar yadda wata sanarwa da sakatarensa, Farfesa Isa Hayatu Chiroma, SAN, ya sanya wa hannu ta bayyana.
Rahotanni sun ce waɗanda suka tsira daga lamarin sun danganta mutuwar da tsananin zafi da suka ce ya addabe su a cikin ɗakin da aka tsare su.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa an kama tare da tsare kimanin matasa 60 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne ba bisa ƙa’ida ba a wani ɗakin tsarewa na NSCDC, inda daga bisani 37 daga cikinsu suka rasa rayukansu.


No comments