BBC Za Ta Rufe Wasu Tashoshinta Saboda Matsalar Kuɗi
Daga Aliyu Saleh
Darakta Janar na BBC, Matt Brittin, ya ce matsin tattalin arziƙin da suke fuskanta da kuma sauyin yadda jama’a ke kallon shirye-shirye na iya tilasta wa BBC rufe wasu tashoshin talabijin da gidajen rediyo, domin mayar da kuɗaɗen wajen gudanar ayyukan da ake amfani da su ta hanyar Intanet.
Yayin da ake hira da shi a shirin Sunday With Laura Kuenssberg na BBC One, Brittin ya ce hukumar na neman rage kashe kuɗaɗe da suka kai kusan Fam miliyan 500.
Ya ce ba za a iya tabbatar da cewa wani shiri ko wata tasha za ta ci gaba da wanzuwa har abada ba, saboda halin kuɗaɗen da BBC ke fuskanta, wanda haka ya tilasta mata sake duba wasu matakai tun da wuri tun kafin a yi haihuwar guzuma.
Ya ce yadda masu sauraro da masu kallon BBC ke amfani da kafafen watsa shirye-shiryen na sauyawa cikin sauri, musamman yadda mutane ke ƙara kallon shirye-shirye a lokacin da suka ga dama.
Ya bayar da misalin wata tasha da mutane 100,000 ke kallon shirye-shiryenta kai tsaye, yayin da wasu 500,000 ke kallon shirye-shiryen ta hanyar iPlayer, yana mai cewa BBC za ta duba lokacin da ya dace ta mayar da irin waɗannan ayyuka gaba ɗaya zuwa tsarin kallon shirye-shirye a lokacin da mutum ya ga dama.
Brittin ya ce manufarsa ta tsuke bakin aljihun ita ce rage tasirin matakan ga masu sauraro, tare da tabbatar da cewa masu biyan kuɗin da ake bai wa BBC sun ci gajiyar kuɗinsu.
Ya ce hukumar ba za ta ci gaba da dogaro da tsohon tsarin yadda mutane ke amfani da kafafen yaɗa labarai ba, domin masu sauraro sun riga sun koma amfani da hanyoyin zamani.
A cikin 'yan watannin nan, BBC ta sanar da soke wasu shirye-shirye da rage guraben ayyuka, ciki har da Blankety Blank, Celebrity Mastermind, Live At The Apollo da Football Focus, yayin da ake sa ran ƙarin ganin wasu shirye-shiryen da za a rage nan ba da jimawa ba.
Brittin, wanda ya zama Darakta Janar na BBC a watan Mayu bayan shafe shekaru 10 yana shugabantar Google a Turai, Gabas ta Tsakiya da Afirka, ya kuma ce BBC na son gwada amfani da fasahar AI wajen samar da shirye-shirye, amma bisa wasu ƙa’idoji.
Ya ce fasahar za ta iya taimakawa wajen rage kuɗaɗen da ake kashewa na gudanarwa da kuma inganta yanke shawara da ƙirƙire-ƙirƙire, amma bai kamata ta maye gurbin basirar ɗan Adam ba, domin shi ya yi imanin cewa ƙirƙire-ƙirƙiren mutane na da muhimmiyar rawa da za ta taka.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ƙananan kamfanonin fasaha na iya samun iko mai yawa kan bayanai, musamman yayin da fasahar AI ke samun ci gaba cikin sauri.
A cewarsa, akwai yiwuwar kamfanoni shida su mamaye hanyoyin samar da bayanai nan gaba, kuma babu ko ɗaya daga cikinsu da ke Turai ko Birtaniya.
Ya ce BBC, wadda fiye da mutane rabin biliyan ke kallon ta a matsayin amintacciyar kafar samun labarai, ya kamata ta zama wata madogara da za ta ba jama'a damar samun bayanai ba tare da dogaro da tsarin 'algorithm' na manyan kafafen samar da bayanai na kasuwanci ba.


No comments