Breaking News

Mata Sun Lashi Takobin Goyon Bayan Tinubu Da Uba Sani A 2027

Daga Hadi Bawa 

Mata a jihar Kaduna sun ƙara bayyana aniyarsu ta goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a zaɓen 2027, domin ci gaba da manufofin raya ƙasa da suka faro a jihar.

Wakilin TNL Hausa ya ruwaito cewa, matan sun bayyana hakan ne yayin wani taro da ƙungiyar 'Arewa Women for Tinubu and Uba Sani Renewed Hope Agenda' ta shirya a Sabon Gari, Zariya, ƙarƙashin jagorancin Kwamishiniyar Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Hajiya Sa’a Garba Dogon Bauchi.

Taron ya haɗa mata, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, wakilan al’umma, magoya baya da sauran ’yan ƙasa masu kishin ci gaba, domin tattauna batutuwan shugabanci nagari, haɗin kai, ci gaba da dorewar manufofin gwamnati.

A yayin taron, mahalarta sun tattauna nasarorin da ake dangantawa da shirin Sabunta Fata na Shugaba Tinubu, da kuma ƙoƙarin canza fasalin jihar Kaduna da Gwamna Uba Sani ke yi ba dare ba rana.
Haka kuma, taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa wayar da kan jama’a tun daga tushe da kuma ƙara shigar mata cikin harkokin siyasa, la’akari da rawar da suke takawa wajen ci gaban al’umma, daidaiton iyali da gina ƙasa.

Mahalarta taron da muka zanta su, sun yaba wa Hajiya Sa’a Garba Dogon Bauchi, wadda ta shirya taron, inda suka ce ƙoƙarinta na haɗa mata da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da wayar da kai ta cancanci yabo da ƙarfafawa.

Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, mahalarta sun jaddada muhimmancin haɗin kai, zaman lafiya, shiga harkokin siyasa cikin sanin ya kamata da kuma wayar da kan jama’a domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na 'yan ƙasa.

No comments