Breaking News

Me Ya Sa Christopher Musa Ya Goyi Bayan Tinubu Da Uba Sani A Zaɓen 2027?

Daga Hadi Bawa 

Ministan tsaro na Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, a zaɓen 2027 mai zuwa.

TNL Hausa ta ruwaito cewa, Musa ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin ƙananan hukumomi na GCG Musawah 4 PBAT 2027, wata ƙungiyar da ke gudanar da gangamin wayar da kan jama’a da tallata Tinubu a Kaduna. 

Ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su ƙara himma wajen gudanar da ayyukan neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu da Uba Sani.

Taron ya bai wa ministan damar tattaunawa da masu yaɗa manufofin siyasa daga ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, da kuma wakilan ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki sama da 300 da ke ƙarƙashin ƙungiyar.

A cewar wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, James Swam ya fitar, Musa ya jaddada muhimmancin haɗin kan jama’a da sadaukar da kai wajen gina Najeriya mai ƙarfi da wadata.

“Zan ci gaba da aiki tuƙuru domin ganin Najeriya ta samu nasara. Ya kamata mu ci gaba da jajircewa wajen gina wannan ƙasa, domin idan muka haɗa kai, za mu fi ƙarfi a matsayin al’umma,” in ji Musa.

Ministan ya kuma jaddada muhimmancin haƙurin da juna bisa bambancin addini, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin al’ummomi, yana mai cewa abubuwan da ya gani tun yana ƙarami a Sakwato sun koya masa sanin muhimmancin rayuwa tare da mutane masu addinai daban-daban.

Ya ce, “Na girma a Sakkwato, don haka babu yadda zan ƙi wani addini.” Musa ya kuma tuna yadda a lokacin ƙuruciyarsa yake shiga bukukuwan Sallah tare da abokansa da maƙwabtansa Musulmi.

“Na tuna a lokacin Sallah, mu yara ne muke riƙe da ragon layya da za a yanka,” in ji shi.

Musa ya ce Najeriya na da ɗimbin albarkatun ɗan Adam da na ƙasa waɗanda za su iya sauya makomar ƙasar idan ’yan ƙasa suka haɗa kai tare da jajircewa wajen cimma burin ci gaban ƙasa.

Ya ce, “Allah Ya sanya mu a Najeriya ne domin mu gina wannan ƙasa, kuma muna da ƙarfin yin hakan, ta fuskar albarkatun ɗan Adam da kuma na ƙasa.”

Ministan ya buƙaci ’yan Najeriya su ɗauki gina ƙasa a matsayin nauyin da ya rataya a wuyansu baki ɗaya.

No comments