BRICS Ta Yi Allah-wadai Da Hare-haren Soji Ba Tare Da Dalili Ba
Daga Fatima Aliyu
Shugabannin ƙasashe 11 da ke cikin ƙungiyar BRICS sun amince da wata sanarwar haɗin gwiwa da ke yin Allah-wadai da amfani da ƙarfin soji ba tare da amincewar ƙasa da ƙasa ba, da kuma hare-haren da ba a tsokane su ba, ba tare da ambaton wata ƙasa kai tsaye ba.
Sanarwar ta kuma yi kira da a tabbatar da zaman lafiya a yankuna, da kare fararen hula da muhimman ababen more rayuwa, tare da yin adawa da amfani da ƙarfi ko barazanar amfani da shi.
Haka kuma, ta jaddada muhimmancin tattaunawa, diflomasiyya da ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa.
An cimma matsayar ne ranar Asabar bayan shafe lokaci ana tattaunawa a wani zama na sirri da ƙasashen da suka kafa ƙungiyar BRICS suka gudanar, a daidai lokacin da taron ƙungiyar na shekarar 2026 ya fara a cibiyar Bharat Mandapam da ke New Delhi, babban birnin Indiya.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, inda ƙasashen BRICS ke ƙoƙarin inganta tattaunawa da rage zafin rikice-rikicen yankin.
Taron na kwanaki biyu, wanda aka gudanar daga 12-13 ga Satumba, ya gudana ne ƙarƙashin taken “Gina Ƙarfi, Ƙirƙire-ƙirƙire, Haɗin Kai mai Ɗorewa.”
Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar sun haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta Kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da ƙasashen abokan hulɗa da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da aka gayyata.
A yayin taron, shugabannin ƙasashen sun kuma tattauna batutuwan zaman lafiya, kasuwanci, makamashi, haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da kuma kare hanyoyin samar da kayayyaki, a daidai lokacin da ake fuskantar yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen siyasa a sassa daban-daban na duniya.
Ƙasashen BRICS sun yi kira da a tabbatar da zaman lafiya da kauce wa ɗaukar matakan da za su ƙara ta’azzara rikicin Yammacin Asiya.
Haka kuma, sun bayyana buƙatar ƙarfafa muryar ƙasashe masu tasowa a manyan cibiyoyin kuɗi na duniya, ciki har da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.
Najeriya na halartar taron a matsayin ƙasa abokiyar hulɗa ta BRICS, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ke wakiltar ƙasar.
Ana sa ran Shettima zai yi amfani da damar taron wajen neman hanyoyin jawo.masu zuba jari daga ƙasashen waje da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziƙi, musamman a fannonin noma, fasaha da sauran ɓangarorin da ba na man fetur ba.


No comments