El-Rufai Na Girbar Abin Da Ya Shuka Ne -Shehu Sani
Daga Aliyu Saleh
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana fuskantar sakamakon abin da ya bayyana a matsayin rashin kyakkyawan shugabanci da kuma yadda ya gudanar da mulki a lokacin da yake kan kujerar gwamna.
Sani ya ce El-Rufai bai mutunta tsarin bin doka ba a lokacin mulkinsa, yana mai zargin cewa tsohon gwamnan ya kama tare da tsare mutane da dama a jihar ba bisa ƙa'ida, don yana girbar abin da ya shuka ne.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today a daren Juma’a da TNL HAUSA ta gani, inda yake martani kan kalaman El-Rufai na baya-bayan nan cewa abokansa, ’yan'uwansa da tsoffin abokan aikinsa da ya taɓa tsaya musu a baya sun juya masa baya.
A halin yanzu, El-Rufai na tsare bisa umarnin kotu bayan an kama shi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake dangantawa da lokacin da yake mulkin jihar. Waɗannan dai zarge-zarge ne da ke gaban hukumomin shari’a.
Sani ya ce: "Yanzu ya kwashe kusan kwanaki 200 a tsare. Ni da na taɓa zama a gidan yari tsawon shekaru huɗu, ba na ganin wani zai iya yi min wa’azi kan tsarewa da raɗaɗin zaman gidan yari. Amma ɗabi’a ce cewa idan mutum ya fita daga cikin harkokin jama’a na wani lokaci, dole ne ya rasa wasu abokai."
El-Rufai yana girbar sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da rashin sauke nauyin da ya hau kansa a lokacin da ludayinsa ke kan dawo.”
Sani ya ƙara da cewa ya ji mutane da dama suna nuna tausaya wa El-Rufai, amma ya kamata duk mai riƙe da muƙamin gwamnati ya tuna cewa tamkar kujerar aski ce, wato dama ce ta ɗan lokaci.
A cewar sa, El-Rufai ya kasance kan mulki ne a lokacin da, yake ganin bai ya kamata ya mutunta tsarin doka ba, kuma ya zargi tsohon gwamnan da rashin bin umarnin kotuna, tare da kama mutane da dama da tura su gidan yari.
“Yau, ya tsinci kansa a wurin da ya kai mutane da dama,” in ji Sani.
Ya ƙara da cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023, Kaduna ta tsinci kanta cikin matsalolin shugabanci da kuma amfani da iko wajen tursasa wa abokan hamayya da tsare su.
Kalaman Sani sun zo ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan tsarewar da ake yi wa tsohon Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai da kuma zarge-zargen da ake yi masa.
Lauyoyin tsohon gwamnan sun sha musanta wasu zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da cewa wasu daga cikin zarge-zargen ba a tabbatar da su a gaban kotu ba.


No comments