Yadda Rikicin Siyasa Ya Raba Gidan El-rufa’i
Daga Wakilinmu
Abin da ke faruwa a tsakanin ’ya’yan gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ba wai kawai batun Bello da kusancinsa da Gwamna Uba Sani ba ne. A’a, abin ya fi haka zurfi.
Yanzu tambayar ita ce: Shin gadon siyasar El-Rufa’i zai ci gaba da zama gado guda ne, ko kuwa kowane ɗa zai ɗauki nasa ya nufi wata hanya?
Domin a siyasar Najeriya, ko da gida guda ake zaune, idan siyasa ta shiga ƙofar gida, wani lokaci sai an fara neman wanda ya fi cancanta ya zauna a kujerar “aminin baba”.
Ga alama gidan El-Rufa’i ma ya fara samun irin wannan taron dangi na siyasa, amma maimakon a zauna a ɗakin taro da shayi ana hira da musayar bayanai cikin raha, sai aka zauna a X, kowa ya ɗauki waya yana kai wa ɗan’uwansa mummunan farmaki.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda rikicin da ya fara tsakanin tsohon Gwamna El-Rufa’i da magajinsa, Uba Sani, ya koma wani sabon salo da ya shafi ’ya’yansu. Wato iyaye sun yi saɓani, yanzu yaran suna farmakar juna tare da jifan juna da kalaman ɓatanci da bayyana ra’ayoyin da suka yi hannun riga da juna.
Tambayar da ake yi ita ce: Wai dama ba a samun saɓani a tsakanin ’yan’uwa? Ko kuwa dai rikicin kishiyoyi ne yake neman rikiɗewa zuwa husumar kamar ta ’yan ubanci? Amma abin mamakin shi ne; Bello da Bashir wa da ƙani ne uwa da uba ɗaya.
Husuma ce mai tsananin gaske, wadda duk lokacin da aka tattauna a kan wata matsala a tsakanin iyalan tsohon Gwamnan, mutane suna karanta sakamakon bayan taron ne a shafukan sada zumunta.
A yayin da shugaban wannan iyalin, wanda ya jagoranci jihar Kaduna mai mutane sama da miliyan shida tsawon shekaru takwas, yake cika kwanaki 200 a tsare a hannun ICPC, su kuma suna nan suna farmakar juna tare da jifan juna da miyagun kalamai.
Amma duk da takaicin da ke cikin lamarin, bai kamata a kalle shi kawai a matsayin faɗan ’yan uba a kafafen sada zumunta ba.
Irin kalaman da Bashir ya jefi Bello da su na nuna irin halin da jama’ar Mazaɓar Kaduna ta Arewa, waɗanda suka zaɓe shi suka tura shi Majalisar Wakilai domin ya wakilce su, za su iya shiga cikin wannan muhawara.
Jifan Bello da ake yi wa laƙabi da “jiƙa hanta”, da miyagun kalaman da Bashir ya yi, ya sake buɗe wani sabon shafi na sake nazari kan wanda jama’a za su zaɓa domin ya wakilce su. Domin shaidar ɗan’uwa ga ɗan’uwansa ta fi ta waninsa tasiri.
Bello ɗan siyasa ne da yake da nasa tsarin tafiyar siyasa da kuma mutanen da ke mara masa baya. Yana ƙoƙarin gina kansa a fagen siyasa, kuma ya nuna cewa idan akwai abin da yake son faɗa, ba lallai sai an kira taron manema labarai ba; shafin X ya isa!
Wannan ya sa abin ya wuce wasan barkwanci, domin abin da ake gani na iya zama farkon wani sabon yanayi a siyasar gidan El-Rufa’i.
Gaskiyar magana ita ce, siyasar Kaduna ta riga ta ga yadda abota da gaba ke canza kaya kamar rigar sanyi a lokacin zafi. Wanda yake abokin tafiya yau, gobe yana iya zama abokin gaba, ana raba faɗa a kafafen sada zumunta. Wanda ake zargi da cin amana yau, gobe kuma ya bayyana a matsayin “fitaccen abokin tafiyar siyasa”.
Najeriya ma tana da ƙamus na siyasa mai sauƙun fahimta sosai; abokin jiya na iya zama abokin gaba na yau, makiyin yau kuma ya zama abokin tarayya na gobe. Yanzu kuma ’yan’uwa ma suna iya fitowa su girji bakin juna a bainar jama’a.
Babbar tambayar da ke bayan wannan cacar baki ita ce: Waye ya mallaki sunan da gadon siyasar El-Rufa’i? Shin uban ne? ’Ya’yansa ne? Tsofaffin abokan siyasa ne? Mutanen da suka amfana da mulkinsa ne? Ko kuwa waɗanda har yanzu suke ganin falsafarsa ta siyasa ita ce mafita?
Abin da ke faruwa tsakanin Bashir da Bello bai kamata a tsaya kan dariya da shagube kawai ba. Ya kamata a duba shi a matsayin yadda siyasa za ta iya raba abin da jini ya haɗa. Tambayar ita ce: Me zai rage daga ginin siyasar da El-Rufa’i ya kwashe shekaru yana ginawa, idan wanda ya kafa tsarin ba ya cikin gidan gwamnati?
Don haka, duk wanda yake ganin musayar waɗannan zafafan kalamai a matsayin wasan kwaikwayo ko barkwanci, wataƙila yana kallon labarin ne daga teburin mai shayi, bai dubi rikicin da irin madubin da jaridar TNL Hausa take kallonsa ba.


No comments