Me Shugabannin Izala Suka Je Yi A Birtaniya?
Daga Aliyu Saleh
Tawagar Da’awa ta Ƙungiyar Izala ta isa ƙasar Birtaniya ta ƙara samun ƙarfi, bayan isowar Shugaban Kwamitin Da’awa na ƙungiyar, Sheikh Dr. Yakubu Musa Hassan Katsina, birnin London a ranar Juma’a domin haɗuwa da manyan malaman ƙungiyar da ke jagorantar ayyukan da’awa a ƙasar.
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya isa London ne domin haɗuwa da Shugaban ƙungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Sheikh Kabiru Haruna Gombe, tare da sauran ’yan tawagar da ke gudanar da ayyukan yaɗa addinin Musulunci a Birtaniya.
Ziyarar ta zo ne a matsayin wani mataki na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin malaman da masu gudanar da ayyukan da’awa, da kuma samar da ƙarin hanyoyin da za a bunƙasa yaɗa ilimin Musulunci a tsakanin al’ummar Musulmi da ke zaune a Birtaniya.
Haɗuwar manyan malaman da kuma nuna yadda ake ci gaba da faɗaɗa ayyukan da’awa zuwa ƙasashen Turai, tare da ƙarfafa ilimin addini, tarbiyya da haɗin kan al’ummar Musulmi.
Ana sa ran tawagar za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wa’azi da ilmantarwa a Birtaniya, domin isar da saƙon Musulunci cikin hikima da kyakkyawar mu’amala.
Amma tambayar da jama'a ke yi ita ce, me ya sa ƙungiyar ta zaɓi zuwa Birtaniya a daidai lokacin da kakar zaɓe ke ƙara ƙusantowa?


No comments