Breaking News

Zanga-zanga ta barke a Kano sakamakon cire Dan takarar Jam'iyar NDC


Daga Abdullahi Sambo Richifa.

Daruruwan magoya bayan kwankwasiyya ne suka fito zangazanga sakamakon cire Dan takaransu da hukumar zabe Mai zaman kanta ta INEC ta yi.

Sun fito ne dai dauke da kwalaye mai   rubutu daban-daban suna nuna fishin su game da cire musu dan takara da hukumar INEC din ta yi.
Wanda aka tsayar a matsayin mataimakin dan takaran Gwamna a Jam'iyar NDC din Mustapha Kwankwaso shi ya jagoranci zangazangan. A inda suka je ofishin hukuren INEC din na jihar Kano suka Mika takardan koken su a Yau Juma'a.
Shugaban hukumar zaben jihar Kano, wato Abdu Zango shi ya karbi ta kardan koken. Kuma ya tabbatar musu za'ayi abun da ya da ce akan wannan koke na su.

Da Jaridan TNL Hausa ta tuntubi Baturen zaben ya ce sun yi abun da ya kamata.
Ya ce "dama haka ake so idan abu ya dame mutane to ku su kai korafin su ga hukumar da abun ya shafa   domin daukar mataki". Inji  shi .

No comments