Breaking News

‎Jerin Jihohi 20 da Tinubu ba zai samu damar zuwa kamfen ba

Daga Abdullahi Sambo Richifa 

‎
‎Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓensa a jihohi 12 kacal, yayin da shugabannin jam’iyyar APC za su wakilce shi a jihohi sama da 20 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
‎
‎Jaridar TNL Hausa ta ruwaito cewa jadawalin gangamin da jam’iyyar ta fitar ya nuna cewa za a fara gangamin ne a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoba, 2026, yayin da ake sa ran kammala rangadin gangamin shugaban a Legas ranar 9 ga Janairu, 2027.

‎Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan gangamin yaƙin neman zaɓe ba saboda akwai buƙatar ya daidaita harkokin siyasa da nauyin gudanar da gwamnati.
‎
‎Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce har yanzu akwai nauye-nauyen da yake da alhakin saukewa a wuyansa.
‎
‎Sai dai ya yi alƙawarin samar da lokacin da zai yi magana kai tsaye da ’yan Nijeriya domin neman goyon bayansu a zaɓen 2027.
‎
‎Jadawalin ya nuna cewa Tinubu ba zai halarci gangamin APC a Cross River ranar 2 ga Nuwamba, Gombe ranar 3 ga Nuwamba, Nasarawa ranar 4 ga Nuwamba da Ekiti ranar 5 ga Nuwamba ba.
‎
‎Haka kuma, ba zai halarci gangamin a Ebonyi, Jigawa, Ondo da Edo ba, waɗanda aka tsara gudanarwa tsakanin 9 zuwa 12 ga Nuwamba.
‎
‎Sai dai zai halarci gangamin a jihar Rivers ranar 7 ga Nuwamba, sannan ya koma Plateau ranar 14 ga Nuwamba.
‎
‎Haka kuma, shugaban ba zai halarci gangamin APC a Yobe, Kebbi, Akwa Ibom da Anambra ba, waɗanda aka tsara gudanarwa tsakanin 16 zuwa 19 ga Nuwamba.
‎
‎Zai halarci gangamin a Oyo ranar 21 ga Nuwamba, yayin da aka tsara gudanar da sauran gangamin a Borno ranar 25 ga Nuwamba, Enugu ranar 28 ga Nuwamba da Bauchi ranar 29 ga Nuwamba.
‎
‎Za a ci gaba da gangamin a watan Disamba, ciki har da Sokoto ranar 5 ga Disamba, Delta ranar 12 ga Disamba da Kano ranar 17 ga Disamba.

No comments