Breaking News

Pantami Da Gwarzo Sun Tsallake Siraɗin INEC

Daga Hadi Bawa 

Alamu sun nuna cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da ci gaba da takarar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, na jam’iyyar PDP a jihar Gombe, da Abdulsalam Gwarzo na jam’iyyar NDC a jihar Kano bayan sun tsallake siraɗinta, duk da kuwa akwai shari’o’in da ke gabansu a kotu.

TNL Hausa ta fahimci cewa cire sunayen 'yan takarar ya jefa damuwa a zukatan magoya bayansu, yayin da sanarwar dawo da su da INEC ta yi ya jefa farin ciki da annuri.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta ɗauki matakin ne a wani taronta da ta gudanar ranar Alhamis, inda ta duba ƙorafe-ƙorafen jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da ba a saka sunayensu cikin jerin sunayen ’yan takarar da aka fitar gabanin zaɓen shekarar 2027 ba.

Wata majiya ta bayyana cewa INEC ba ta da ja kan takarar mutanen biyu, sai dai har yanzu ana jiran sakamakon wasu shari’o’in da ke gaban kotuna, waɗanda za su iya shafar matsayinsu na ƙarshe.

A jihar Kano, INEC ta amince da Abdulsalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC, inda ta tabbatar da cewa ya cika sharuɗɗan da ake buƙata domin tsayawa takarar zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027. 

Tuni aka sanarwa amincewar ta hanyar wasiƙar da aka miƙa wa shugabancin jam’iyyar NDC a  Kano ranar Alhamis.

Gwarzo, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwamna a jihar Kano, ya samu wannan ci gaba ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Magoya bayansa sun bayyana amincewar a matsayin wani mataki ga burinsu na ƙwace ragamar mulkin jihar daga hannun APC.

A ɓangaren jihar Gombe kuwa, Pantami, wanda ya samu tikitin takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC a ranar 19 ga Mayun 2026, ya fuskanci ƙalubale bayan Ahmed Mailantarki, ɗaya daga cikin masu neman tikitin jam’iyyar, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar nasararsa.

Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwani na farko tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da shi, inda Pantami ya sake samun nasara. Sai dai babban ƙalubalen da ya fuskanta shi ne hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumban 2026, wanda ya kalli wasu sassan dokar zaɓe ta shekarar 2026 da suka shafi rajistar ’yan jam’iyya da kuma cancantar tsayar da ’yan takara.

Rahotanni sun ƙara da cewa, bayan bayyanar labarin yiwuwar amincewar INEC ga Pantami, magoya bayansa sun fito kan manyan tituna da wuraren taruwar jama’a a Gombe a daren ranar Alhamis domin murnar wannan nasarar da suka ce sun samu.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an INEC ba su mayar da martani kai tsaye kan tambayoyin da jaridar Vanguard ta aika musu game da lamarin ba. Saboda haka, ana buƙatar ƙarin tabbaci daga hukumar kan cikakkiyar amincewa da ’yan takarar biyu da kuma tasirin shari’o’in da ke gabansu.

No comments