NAWIA Ta Buƙaci Tallafawa Mata Manoma a Zamfara
Daga Zainab Idris Bamalli
Ƙungiyar Mata Manoma ta Najeriya (NAWIA), reshen Jihar Zamfara, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta jiha, da Bankin Aikin Gona da abokan hulɗar ci gaba, da su ƙara tallafa wa mata manoma domin bunƙasa samar da abinci.
Shugabar ƙungiyar ta jihar, Hajiya Shemau Muhammad Nalado, ce ta bayyana hakan yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta 2026 da aka gudanar a Gusau, inda ta ce ƙungiyar na da mambobi sama da 3,000 da ke noma shinkafa, gero, gyada, kayan lambu da kiwon kaji.
Ta bayyana cewa mata manoma na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da rashin samun lamuni, kayan aikin noma na zamani, wuraren sarrafa amfanin gona da kuma sauyin yanayi.
A nata jawabin, Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na bunƙasa noma da ƙarfafa mata.
Shi ma Manajan Shirye-shiryen NAWIA na jihar, Ukashat Bashar Anka, ya bayyana cewa ƙungiyar ta horas da mata sama da 2,200 a shekarar 2026 kan hanyoyin inganta noma da sarrafa amfanin gona.
Ya kuma yi kira da a samar da cibiyar sarrafa amfanin gona ta mata a Gusau, tare da shigar da su cikin shirye-shiryen tallafin noma na gwamnati.


No comments