Naira Miliyan 100 Ta Jawo Ce-ce-ku-ce Tsakanin Jaruma Da Jami’in Tsaron Seyi Tinubu
Daga: Hauwa’u Maikudi
Wani jami’in tsaron Seyi Tinubu, Olawale Dare, ya zargi fitacciyar ’yar kasuwa Hauwa Saidu Mohammed, wadda aka fi sani da Jaruma, da neman kuɗi har naira miliyan 100 tare da yi masa barazanar fallasa sirrin abin da ya ce ya faru tsakaninsu.
A cewar rahoton S-Media Nigeria, Dare ya gabatar da waɗannan zarge-zarge ne a cikin bayanin da ya bayar ga Cibiyar Yaƙi da Laifukan Intanet ta Rundunar ƴan Sandan Najeriya (NPF-NCCC) a ranar 8 ga Oktoba, 2026.
Dare ya ce sun haɗu da Jaruma a Abuja a ƙarshen shekarar 2025 ta hannun wani abokinsu. Ya bayyana cewa bayan sun fara hulɗa, Jaruma ta nemi ya zuba jari a kasuwancinta na kayayyakin mata.
A cewarsa, Jaruma ta nemi ya ba ta tsakanin naira miliyan 100 zuwa miliyan 200, tare da alƙawarin mayar masa da kuɗin da ƙarin riba, amma ya ce bai amince da tayin ba.
Ya ƙara da cewa daga baya Jaruma ta sake neman taimakon kuɗi daga gare shi, inda ya ce ya ba ta kuɗi tsakanin naira 30,000 da 40,000.
Babban zargin da Dare ya yi shi ne cewa Jaruma ta yi barazanar sanar da Seyi Tinubu game da hulɗar da ta kasance tsakaninsu, tare da neman naira miliyan 100. Haka kuma, ya yi zargin cewa ta yi barazanar zarginsa da fyɗe, tana mai cewa tana da mata 12 da za su iya bayar da shaida a kansa.
Dare ya ce bai kai rahoton lamarin ga ƴan sanda nan take ba saboda shawarar da abokansa suka ba shi.
TNL HAUSA


No comments