Mawaƙan TUSCOF Sun Karɓi Baƙuncin Babban Sakataren Ƙungiyar TUSCOF
Babban Sakataren ƙungiyar TUSCOF, Hon Ibrahim Ibrahim ya kai ziyarar gani da ido ga Kungiyar Mawaƙan TUSCOF a cikin garin Kaduna.
Yayin da yake miƙa godiya ga Sakataren, shugaban kungiyar ta Mawaƙan TUSCOF, Alhaji Sagir Baban Kasar, ya jinjina, tare da yi wa Hon Ibrahim godiya bisa ziyarar, inda ya tabbatar da shirye-shiryen Mawaƙan na TUSCOF wajen ba da gudunmawa da himmar ganin Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da Mai Girma Sanata Ina Sani, da kuma jam'iyyar APC sun samu gagarumar nasara a zaɓuka masu zuwa na 2027.
Wakilinmu ya ce Baban Kausar ya kuma yi amfani da wannan damar wajen miƙa saƙon godiyarsu ta musamman ga Mai Gayya mai Aiki, kuma jagoran wannan tafiya ta Ƙungiyar TUSCOF, Shugaban Ma'aikatar Fadar Gwamnatin Jihar, Alhaji Sani Liman Kila MFR, bisa gudummuwa mai kauri da ya aika mu su, ta hannun Babban Sakataren na TUSCOF Hon. Ibrahim.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa TUSCOF, haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu rajin tabbatar da nasarar shugaban ƙasa da gwamnan Jihar Kaduna a zaɓe mai zuwa na 2027.
An dai kafa ƙungiyar ne a Jihar Kaduna domin ci gaba da wayar da kan al'umma dangane da nasarorin da jam'iyyar APC ta samar, tare yin kira ga al'umma su marawa shugaban ƙasa da Gwamna Uba Sani domin ci gaba da samun romon dimokuraɗiyya.


No comments