Malaman Musulumci Sun Karrama Pasto Buru Bisa Shekaru 25 Na Kokarin Samar Da Zaman Lafiya
Daga Zainab Idris Bamalli
Malaman addinin Musulunci a jihar Kaduna sun karrama Fasto Dr. Yohanna Buru, inda suka ba shi sarautar girmamawa ta “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”, bisa jajircewarsa na tsawon shekaru 25 wajen inganta zaman lafiya, fahimtar juna da kuma haÉ—in kai tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Babban Limamin Madarasatul Sheikh Usman Muhammad Mai Mota Gwalli da ke Kaduna ne ya jagoranci tawagar fitattun malaman Musulunci zuwa cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Bagyi Villa, Kaduna, domin karrama Fasto Buru bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Sheikh Usman Muhammad Mai Mota Gwalli ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da kuma karrama faston bisa ƙoƙarinsa na yaɗa zaman lafiya, yafiya, soyayya, haɗin kai da kuma kyautatawa al'umma ba tare da la'akari da ƙabila, al'ada ko yankin da mutum ya fito ba.
Ya ce Fasto Buru ya taka muhimmiyar rawa wajen haÉ—a kan al'ummomi da kuma inganta fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar Kaduna da sauran sassan Najeriya.
Sheikh Usman ya kuma bayyana cewa Fasto Buru ya samu kyautar World Interfaith Harmony Week ta Majalisar ÆŠinkin Duniya, wadda Sarki Abdullah na biyu na Jordan ya ba shi, saboda gudummawarsa wajen inganta fahimtar juna tsakanin addinai.
Fasto Buru, wanda ya samu kyaututtuka sama da 20 na zaman lafiya da ayyukan jin ƙai, ya shafe shekaru yana ƙoƙarin samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, fahimtar juna da haɗin kai tsakanin al'ummomi masu bambancin addini, ƙabila da al'adu.
Da yake mayar da martani, Fasto Dr. Yohanna Buru ya nuna godiyarsa ga tawagar malaman Musulunci bisa ziyarar da suka kai masa a cocinsa da kuma karrama shi yayin da yake bikin cika shekaru 25 yana gudanar da ayyukan samar da zaman lafiya a Najeriya da sauran sassan Afirka.
Ya bayyana cewa wannan lokaci wani muhimmin mataki ne a tafiyarsa ta samar da zaman lafiya, wadda ta haɗa da ziyartar ƙasashe daban-daban domin koyon hanyoyin da al'ummomi ke amfani da su wajen rayuwa cikin lumana duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Fasto Buru ya ce ya ziyarci ƙasashe da dama a cikin Afirka da wajen nahiyar domin koyon yadda mutane ke rayuwa cikin zaman lafiya da jituwa duk da bambancin ƙabila, al'ada, kabila da addini.
Ya bayyana cewa ya yi amfani da darussan da ya koya daga waɗannan ƙasashe wajen gudanar da ayyukansa na samar da zaman lafiya a Najeriya, ta hanyar shirya tattaunawa da ƙarfafa mutunta juna tsakanin al'ummomi.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya na buƙatar ci gaba da tattaunawa, fahimtar juna da kuma ɗaukar matakai na zahiri domin haɗa kan mutane masu bambancin addini da al'adu.
Fasto Buru ya kuma bayyana cewa a cikin shekaru 25 da ya shafe yana wannan aiki, ya horas da É—aruruwan matasa a matsayin jakadun zaman lafiya a faÉ—in jihohin Arewa 19 na Najeriya.
A cewarsa, matasan da aka horas ɗin suna taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa haƙuri da juna, hana rikice-rikice da kuma ƙarfafa zaman lafiya a cikin al'ummominsu.
Ya bayyana matasan a matsayin shugabannin gobe waɗanda gudummawarsu za ta taimaka wajen dorewar zaman lafiya da ƙarfafa dangantaka tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.
Fasto Buru ya kuma gode wa dukkan mutanen da suka tallafa masa a wannan tafiya ta samar da zaman lafiya, musamman shugabannin addinai da al'umma waÉ—anda suka ci gaba da ba da gudummawa wajen inganta tattaunawa da fahimtar juna.
A ƙarshe, ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su ci gaba da zama lafiya da juna, su mutunta akidun addinan juna tare da haɗa kai wajen gina Najeriya mai haɗin kai da zaman lafiya.
Ya jaddada cewa bambance-bambancen addini da al'adu bai kamata su zama sanadin rarrabuwar kawuna ba, illa su zama wata dama ta ƙara ƙarfafa mutunta juna, fahimtar juna da haɗin kan ƙasa.


No comments