Limamin Katolika Ya Rasu Bayan Wani Abu Ya Faɗo Masa Yayin Ibada A Ecuador
Daga: Nasir Hassan
Wani limamin cocin Katolika, Father Patricio Sánchez Molinari, ya rasu bayan wata babbar gicciye ta katako ta faɗo masa a kai yayin gudanar da ibada a cocin Our Lady of Perpetual Help da ke birnin Guayaquil, a ƙasar Ecuador.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da ake gudanar da ibadar Mass, wadda ake watsawa kai tsaye ta kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa limamin yana gaban bagadi lokacin da Koros wanda aka rataye a bango a bayansa, ya kuɓuce ya faɗo masa a kai.
Bayan faruwar lamarin, masu ibada sun garzaya domin taimaka masa tare da kiran motar asibiti.
Daga bisani, babban ofishin cocin Katolika na Guayaquil ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya bayyana cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar addini ta Redemptorists.
Cocin ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga ƴan'uwa da abokan arzikin marigayin.
Ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, ba a bayyana a hukumance musabbabin kuɓucewar gicciyen daga bangon ba.
Majiya: Associated Press (AP) da El Universo.
Fassara: Hauwa'u Maikudi


No comments