Breaking News

Ƙasashen Najeriya Da Uganda, Na Neman Tikitin Zuwa Matakin Gaba Na Neman Gurbin Gasar Cin Kofin Duniya Ta T20


Daga Hauwa'u Maikudi

Ƙasashen Najeriya da Uganda sun bayyana aniyarsu ta samun gurbi a matakin gaba na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kiriket na T20 ta shekarar 2028, yayin da shugabannin ƙungiyoyin suka gargaɗi 'yan wasansu kan yin sakaci.

Gasar neman gurbin, wadda za a gudanar a Abuja daga ranar 18 zuwa 26 ga Oktoba, 2026, ta ƙunshi ƙasashe shida da suka haɗa da Najeriya, Uganda, Zambia, Lesotho, Mozambique da Gambiya.

Ƙungiyoyin za su fafata a tsarin da kowace ƙasa za ta kara da sauran, inda ƙasashe biyu na farko za su samu gurbin shiga matakin ƙarshe na neman cancantar shiga gasar Afirka ta shekarar 2027.

Kocin Uganda, Steve Tikolo, ya bayyana cewa ƙungiyarsa na burin lashe gasar, ba wai samun gurbin zuwa mataki na gaba kawai ba.

Shi ma kyaftin ɗin Uganda, Riazat Ali Shah, ya jaddada muhimmancin mayar da hankali da kuma taka leda yadda ya kamata, yana mai cewa bai kamata ƙungiyar ta raina kowace abokiyar hamayya ba.

A nata ɓangaren, Najeriya za ta yi amfani da damar buga gasar a gida wajen ƙoƙarin samun gurbin zuwa mataki na gaba.

Za a kammala fafatawar da wasan da ake sa ran Najeriya za ta kara da Uganda a ranar 25 ga Oktoba, 2026.

Majiyoyi: ICC da Cricket Uganda.

No comments