Iyalan Matar Da Aka Kashe A Kamfen Ɗin Tinubu Suna Neman Ɗaukin Gwamnatin Kaduna
Daga Hadi Bawa
Wata mata mai suna Laɗifa, matar Musa Mohammed Tudun Nupawa, ta rasu sakamakon raunin da ake zargin ta samu a lokacin da wasu ’yan daba da ba sa ga-maciji da juna suka yi arangama a wajen ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.
TNL Hausa ta fahimci cewa Laɗifa, wadda ta haifi ’ya’ya uku, ta rasu ne washegari a Asibitin Yusuf Ɗantsoho da ke Tudun Wada Kaduna bayan an caka mata wuƙa.
Rasuwarta ta jefa iyaye da iyalanta cikin alhini, inda mijinta ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta taimaka wa iyalin tare da tabbatar da an yi adalci.
Rahotanni sun nuna cewa an caka wa Laɗifa wuƙa a ciki ne yayin da aka samu taƙun saƙa tsakanin wasu da ake zargin ’yan daba ne da mafarauta, waɗanda aka ce yawancinsu sun fito ne daga jihar Kano.
Isyaku Manager Tudun Nupawa, wani abokin mijin marigayiyar, ya shaida wa manema labarai cewa, Laɗifa ta samu mummunan rauni ne a lokacin da waɗanda ke rigimar suke amfani da muggan makamai a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen.
Ya ce, “Yayin da suke amfani da makamai masu haɗari, ɗaya daga cikinsu ya caka mata wuƙa a ciki, wanda hakan ya jawo mata mummunan rauni. Nan da nan aka garzaya da ita asibiti.
"Bayan faruwar lamarin, an ɗora Laɗifa a kan babur domin kai ta asibiti. Sai dai maimakon kai ta asibitin Barau Dikko da ke kusa da wurin taron, sai aka nufi asibitin Yusuf Ɗantsoho. A kan hanyar zuwa asibitin ne ta faɗo daga kan babur sakamakon zubar jini daga raunin da ta samu.
"Bayan isa asibitin, Laɗifa ta shiga cikin mummunan yanayi. Ba ta sake magana har zuwa lokacin da ta rasu da misalin ƙarfe 9 na safiyar Lahadi. Ta rasu ta bar mijinta da ’ya’ya uku ƙanana," in ji shi.
Da yake bayyana yadda ya samu labarin faruwar lamarin, mijin marigayiyar, Musa Mohammed Tudun Nupawa, ya ce ba ya gida a lokacin da aka kira shi ta waya aka sanar da shi cewa matarsa ta faɗo daga kan babur, kuma an kai ta asibiti.
Ya ce bayan ya isa asibitin kuma ya gudanar da bincike, daga baya ne ya gano cewa matarsa ta halarci gangamin yaƙin neman zaɓen APC, inda ta shiga cikin hatsarin da ya biyo bayan arangamar da ake zargin wasu ’yan daba sun yi a tsakaninsu.
“Lokacin da na same ta a asibitin Ɗantsoho, tana kwance a kan gado, amma ba ta iya magana. Haka ta ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da ta rasu,” in ji shi.
Mijin marigayiyar, wanda ya bayyana kansa a matsayin mutumin da ba shi da aikin yi kuma yake ƙoƙarin samar wa iyalinsa abin masarufi, ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi adalci tare da ba su diyya bisa rasuwar matarsa.
Cikin alhini da zubar haway ya ce, “An kashe min mata a wajen gangamin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu. Ta bar ni da ’ya’yana uku. Ina kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi adalci tare da biyan diyya.”
Laɗifa na cikin ɗaruruwan matan da ake zargin an tattaro domin halartar gangamin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.
Bayanan da muka samu sun nuna cewa wasu ’yan siyasa a Kaduna sun aika wa iyalan marigayiyar wasu kuɗaɗe da ba su taka kara suka karya ba da kuma buhunan shinkafa domin taimaka musu a wannan lokaci na alhini.
Duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin jami’an tsaro game da lamarin, haƙa ba ta cimma ruwa ba.


No comments