Breaking News

INEC Ta Bankaɗo Wasu Hotunan Da Ake Zargi Da Fasahar AI Aka Ƙirƙiresu A Rijistar Zaben

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana binciken wasu hotuna da ake zargin an ƙirƙire su ta amfani da fasahar AI, waɗanda suka bayyana a cikin rajistar masu zaɓe ta wucin gadi da ta wallafa a shafinta na intanet.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yaɗa bayanai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar ranar 27 ga Oktoba, 2026, INEC ta bayyana cewa rajistar da ta wallafa a ranar 26 ga Oktoba ita ce wadda aka nuna wa jama'a a cibiyoyin rajista a faɗin ƙasar daga ranar 9 zuwa 15 ga Oktoba.

Hukumar ta ce tun lokacin da aka nuna rajistar ga jama'a, an gano wasu bayanan rajista masu tayar da shakku, waɗanda aka ware domin gudanar da bincike da gyara bisa ƙa'idojin da aka tanada.

INEC ta ƙara da cewa rajistar da aka wallafa a intanet ba ta nuna dukkan gyare-gyaren da ake ci gaba da yi ba, tana mai jaddada cewa rajistar ta wucin gadi ce, ba ta ƙarshe ba.

Ta bayyana cewa manufar nuna rajistar ga jama'a ita ce ba su damar gano kurakurai da rashin bin ƙa'ida, domin a gyara su kafin tabbatar da rajistar ta ƙarshe.

Hukumar ta ce tana kuma binciken yadda hotunan da ake zargin na AI ne suka shiga rajistar, ciki har da yiwuwar samun kura-kurai na fasaha ko na tsarin gudanarwa, kuma za ta ɗauki matakin da ya dace bayan tabbatar da sakamakon binciken.

INEC ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta kammala aikin tantancewa da gyaran bayanan kafin ranar 15 ga Disamba, 2026, wadda aka tsara domin tabbatar da rajistar masu zaɓe ta ƙarshe.

Ta kuma gode wa al'umma da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suka nuna damuwa kan lamarin, tana mai cewa za ta ci gaba da sanar da jama'a duk wani sabon bayani yayin da binciken ke gudana.

No comments