Breaking News

IGP Disu Ya Nemi Ƙarin Kuɗin Alawus Ga Jami’an Ƴan Sanda Masu Ritaya

Daga Hauwa’u Maikudi.

Sufeto-Janar na Ƴan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Disu, ya gabatar da shawarar ƙara kuɗin alawus na ritaya zuwa kashi 200 cikin ɗari, tare da inganta kuɗaɗen fansho ga jami’an Ƴan sanda da suka yi ritaya.

Jaridar Leadership ce ta ruwaito hakan a ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, inda ta bayyana cewa ana nazarin shawarar ne a wani kwamiti da aka kafa domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar tsarin fansho na Ƴan sanda.

Shawarar ta ƙunshi yiwuwar inganta haƙƙoƙin jami’an da suka yi ritaya, ciki har da waɗanda suka yi ritaya kafin fara aiki da sabon tsarin fansho, da kuma duba yadda za a inganta kuɗaɗen fanshonsu bisa la’akari da albashin da suka karɓa na ƙarshe.

Kwamitin da ke nazarin batun ya ƙunshi wakilai daga Ma’aikatar Kuɗi, Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Hukumar Kula da Albashi da Kuɗaɗen Shiga, Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya da Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom).

Matakin na zuwa ne yayin da tsofaffin jami’an Ƴan sanda ke ci gaba da nuna damuwa kan ƙarancin kuɗin fansho, jinkirin biyan haƙƙoƙinsu da matsalolin da suke fuskanta wajen samun kuɗaɗen da suka cancanta bayan barin aiki.

Haka kuma, jami’an Ƴan sandan da ke aiki sun daɗe suna neman a cire rundunar daga tsarin fansho na gudummawa, wato Contributory Pension Scheme (CPS), saboda damuwar da suke nunawa kan yadda tsarin ke shafar kuɗaɗen da suke samu bayan ritaya.


Madogara: Leadership Newspaper.

No comments