Breaking News

Hurras Medical Team Ta Fitar Fa Matakan Kariya Daga Cutar Ebola

Daga Hauwa'u Maikudi 

Ƙungiyar Hurras Medical Team, ƙarƙashin kwamitin wayar da kai na Harkar Musulunci a Najeriya da jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ta fitar da saƙon wayar da kan jama’a kan matakan kariya daga cutar Ebola.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da hukumomin lafiya suka tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja a ranar 20 ga Oktoba, 2026. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an tabbatar da mutum guda da ya kamu da cutar, yayin da mutane 44 da suka yi mu’amala da shi ake sa ido a kansu.

Mene ne cutar Ebola? 

Bincike ya nuna cewa Ebola cuta ce mai tsanani da ke yaɗuwa ta hanyar taɓa jini ko ruwan jikin wanda ya kamu da ita, gawarsa, ko kayayyakin da suka gurɓata da irin waɗannan ruwaye.

Matakan kariya Bisa Ƙa'idar da (WHO) ta sanar

1. Wanke hannu akai-akai

A wanke hannu da sabulu da ruwa, musamman bayan amfani da banɗaki da kafin cin abinci. Idan babu ruwa da sabulu, a yi amfani da sinadarin kashe ƙwayoyin cuta na hannu.

2. Guje wa taɓa ruwan jikin mai cutar

A guji taɓa jini, amai, bayan gida, miyau da sauran ruwan jikin wanda ake zargin ya kamu da Ebola. Kada a kula da mara lafiya ba tare da kayan kariya da horo ba.

3. Guje wa kayayyakin da suka gurɓata

Kada a taɓa tufafi, shimfiɗa, allurai ko wasu kayayyaki da ake zargin sun gurɓata da jini ko ruwan jikin mai cutar.

4. Guje wa taɓa gawar mamaci

A bar ƙwararrun ma’aikatan lafiya su gudanar da ayyukan binne wanda ya mutu sakamakon cutar cikin aminci.

5. Guje wa namun daji masu haɗari

A guji taɓa jemagu, birai ko sauran namun daji da suka mutu ko suke rashin lafiya. Haka kuma, a guji cin ɗanyen naman namun daji ko naman da ba a tabbatar da lafiyarsa ba.

6. Neman taimakon likita

Zazzaɓi, ciwon kai, kasala, amai da gudawa na iya kasancewa cikin alamomin Ebola. Duk wanda ya samu irin waɗannan alamomi bayan yiwuwar hulɗa da mai cutar ya nemi taimakon hukumomin lafiya cikin gaggawa, tare da bayyana tarihin hulɗar.

7. Guje wa jita-jita

A samo bayanai daga hukumomin lafiya da amintattun majiyoyi, kuma a guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba.

Kira ga jama’a

Hurras Medical Team ta yi kira ga jama’a da su kula da tsafta, su bi shawarwarin hukumomin lafiya ta (WHO), kuma su sanar da ma’aikatan lafiya idan sun lura da alamomin da ake zargin na Ebola ne. Kada a dogara da maganin kai ko a ɓoye bayanan da za su taimaka wajen dakile yaɗuwar cutar.

No comments