Apex light Academy Ta Taya Masu shekarun 40-90 Murna zakayowar makon su
Daga Zainab Idris Bamalli
Cibiyar Apex Light Academy ta taya manyan shekarun rayuwa, daga shekaru 40 zuwa 90, murnar Makon Manyan Shekaru (Senior Citizens Week), tare da kira gare su da su kula da lafiyarsu da kuma rayuwa cikin farin ciki.
Cibiyar ta ba da shawarar rage cin gishiri, sukari da abinci da aka sarrafa a masana’antu, tare da yawaita cin kayan lambu, ’ya’yan itatuwa da sauran abinci masu gina jiki.
Haka kuma, ta bukaci masu manyan shekarun da su rika motsa jiki, shan ruwa akai-akai, zuwa duba lafiya, kauce wa rigingimu, kula da iyali da abokai, tare da kasancewa masu kyakkyawan tunani.
Apex Light Academy ta yi fatan kowa zai rayu cikin koshin lafiya, kwanciyar hankali da farin ciki.
Fassara by Zainab idris Bamalli TNL HAUSA


No comments