Harin Binnari: 'Yan Bindiga Sun Kwace Kauyika 9 A Taraba - Inji Tsohon Dan Majalisa Andami
...Ya nemi Gwamnatin Tarayya data kawo wa Gwamna Agbu Kefas dauki
Daga Sule Wakili
Tsohon Dan Majalisa Mai Wakiltan Karim-Lamido ta Biyu a Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Tanko Bobboi Andami ya bayyana damuwa kan yadda 'Yan Bindiga suka hallaka al'umman yankin Binnari dake Karamar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar.
Ya bayyana hakan ne a zantawar su da LMC Hausa ta wayar hannu.
Ya shaida cewa, a halin yanzu akwai kauyika guda tara dake karkashin mallakan 'Yan Bindiga, wanda suka hada da Talajigu, Faskari, Farin ruwa, Komodaro, Gina Rumbu, Jamaga, Mashigin Shivi, da Dukun mai dake da Mazabu (pulling units) guda uku wanda kuma 'Yan Bindigan sun kwashe shekaru biyu suna rike da garin.
Tanko Bobboi Andami ya bayyana cewa, an birne gawan mutane kusan hamsin da daya (51), inda ya zargi cewa 'Yan Bindigan suna shigowa ne daga jihohin Pulato, Bauchi da Kaduna.
Andami wanda kuma shine Dan Masanin Old Muri, ya kara da cewa 'Yan Bindigan sun boye shanun Sata sama da Midiyan Daya a dajin.
"Shanun satan ne suke saidawa suna siyan makamai da sauran harkokin su na ta'addanci," yayi zargin hakan.
Ya roki Gwamnatin Tarayya data maida hankali wajen cigada da aikin hanyar data taso daga Wase na Jihar Pulato zuwa Karim-Lamido na Jihar Taraba, domin magance rashin tsaro.
Yace hanyar kuma zata iya bulla har zuwa Jihar Adamawa.
A cewar sa, idan aka maida hankali wajen cigaba da aikin hanyar, zai taimaka wajen koran 'yan ta'adda a yankin.
Andami, wanda kuma Shine Mai baiwa Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas shawara kan harkokin noman rani, ya yaba da irin matakin da Gwamnatin jihar ta dauka biyo bayan harin da akakai tare da kashe rayukan wasu al'umman garin na Binnari.
"Mai Girma Gwamna Dr Agbu Kefas ya dauki matakan gaggawa da suka hada da tura Jama'an tsaro da kuma Hukumar Bada Agajin gaggawa ya SEMA, inda muka je tare da Shugaban Hukumar aka raba musu kayan abinci da su katifa da tabarmi," inji Andami.
Kazalika ya kuma Shawarci Gwamna Agbu Kefas daya hada kai da takwarorin sa na jihar Pulato da Bauchi wanda suke da iyaka da Karamar Hukumar ta Karim-Lamido don samar da chikakken tsaro.


No comments