Breaking News

Dakarun OPHK Sun Samu Gagarumar Nasara A Ranar ’Yancin Kai, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda, Sun Ƙwato Makamai A Adamawa

Daga Hadi Bawa 

Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun samu gagarumar nasara a jerin samamen da suka kai a tsakanin ranar 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba, 2026 a Jihar Adamawa.

A wata sanarwar da rundunar ta raba wa manema labarai ciki har ta TNL HAUSA, ta bayyana cewa samamen ya haɗa da yi wa 'yan ta'adda kwanton ɓauna ta ƙasa, luguden wuta da jirgin yaƙi da kuma fatattakar ’yan ta’adda, sun kai ga hallaka da dama, tare da ƙwato makamai da alburusai daban-daban da kuma daƙile yunƙurin kai hare-hare kan wuraren da dakarun suke.

A yankin Boima da ke ƙaramar hukumar Gombi, dakarun sun yi wa wata maɓoyar ’yan ta’adda ƙofar rago, inda suka hallaka ’yan ta’adda 16. Bayan kammala arangamar, dakarun sun gudanar da bincike a wurin, inda suka gano bindigogin AK-47 guda uku, bindigogin pump-action guda biyu, bindiga ƙirar Dane guda ɗaya, harsasai masu ɗaukar AK-47 guda shida da kuma bel ɗin harsasan pump-action.
A wani samame da ya biyo baya, rundunar sojin sama ta OPHK ta kai wani hari na musamman da jirgin yaƙi a safiyar 1 ga Oktoba, 2026. Da misalin ƙarfe 4:40 na safe, wani jirgin leƙen asiri da tattara bayanan sirri (ISR) ya gano kusan ’yan ta’adda 16 suna taruwa tare da babura 15 a ƙarƙashin bishiyoyi. 

Bayan tabbatar da sahihancin abin da aka gano, an kai musu hari da misalin ƙarfe 5:30 na safe, inda aka samu nasarar kai musu mummunan hari. 

Binciken da aka gudanar bayan harin ya tabbatar da lalata wurin da aka nufa, yayin da wasu daga cikin waɗanda suka tsira suka watse a firgice.

A lokaci guda, dakarun sun daƙile hare-haren da ’yan ta’adda suka kai kan wuraren da sojojin Bataliya ta 226 da ke Garkida da Bataliya ta 232 da ke Garaha suke. 

Dakarun sun mayar da martani da ƙarfi, inda suka tilasta wa maharan dakatar da harin tare da guduwa. Sai dai, abin takaici, sojoji uku sun rasa rayukansu yayin wannan gumurzu, yayin da aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibiti, inda suke samun kulawar likitoci kuma halin da suke ciki ya daidaita. 

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike da samamen kar ta kwana da katse hanzari a yankunan.

Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da hedikwatar rundunar suke sake fasalin tsarinta domin ƙara haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji, inganta daidaituwar ayyuka da kuma tabbatar da shigar dukkan masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da ta’addanci da tayar da ƙayar baya. 

Rundunar ta ce sabon tsarin yana samar da ƙarin nasarori sakamakon ingantaccen haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasa, na sama da sauran sassan da ke tallafa wa ayyukan.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda, tare da amfani da bayanan sirri, fasaha da haɗin gwiwar rundunoni wajen hana ’yan ta’adda samun damar gudanar da miyagun ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas. 

Yayin da ’yan Najeriya ke bikin cika ranar samun ’yancin kai, dakarun OPHK sun ce za su ci gaba da kare martabar ƙasar da kuma samar da yanayin da zai ba da damar samun zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziƙi a yankin.

Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, ta yaba wa al’umma bisa ci gaba da ba da goyon baya da haɗin kai, tare da yin kira ga jama’a da su kasance cikin shiri tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen karya lagon 'yan ta'adda a yankin.

No comments