Canza Shekar "Yan Majalusun Da A dakatar A Zamfara Zuwa ADC Idan Suka Neman Afuwa Kofarmu Abude Take
-Kakakin Majalisa
Daga Hussaini Yero, Gusau
Sakamakon Canza shekar 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 8 da su kayi bayan sun kwashe watani 30 da dakatar da su ,A Ranar Asabar da tagabata ne suka Canza sheka daga Jamiyyar APC zuwa ADC.
-Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Rt Hon, Bilyaminu Moriki,ya bayyana wa manaima labarai irin laifikan da su kayi wanda ya jawo dakatar da su,daga Majalisar,amma duk da haka kofar Majalisar Abude take ga duk mai neman afuwa akan laifin da sukayi.
Hon Bilyaminu ya bayyana cewa,an dakatar da 'yan majalisar da ake magana a kansu ne a ranar 26 ga Fabrairu 2024, bayan zarge-zargen aikata badakala,rashin ɗa'a, haɗin baki, ɓarna, raina Majalisa, da gudanar da haramtacen zama wanda ya saɓa wa Dokokin tsarin aiki na Majalisa.
Muna zargi waɗannan 'yan majalisar da ayyuka da suka shafi almubazarabci da kudade, shiga da ƙarfi, da lalata dukiyar gwamnati, ciki har da zargin Fasara ofisoshin Akawun Majalisa da na Sajan-at-Arms, da lalata kayayyakin Majalisa, da shiga zauren Majalisa ba bisa ƙa'ida ba, sannan suka gudanar da zaman haram a cikin ta.
Girman waɗannan zarge-zarge da sauran al'amura da ke da alaƙa da su, ya kai ga shigar da ƙarar laifi a gaban kotu mai hurumin shari'a kan 'yan majalisar da aka dakatar.
Dangane da ficewa da waɗannan 'yan Majalisar a kwanan nan, ina so in sanar da ku cewa ƙoƙari ne kawai na karkatar da hankalin jama'a daga ainihin batun ladabtarwa da ke tattare da dakatarwar da aka yi musu da kuma munafincin manufarsu ta nuna cewa Majalisar ba ta da tabbas.
A kan haka, ina so in tabbatar muku da jama'a baki ɗaya musamman magoya bayanmu cewa, Majalisar Dokokin Jiha tana da ƙarfi, tana aiki, kuma tana gudanar da ayyukanta na kundin tsarin mulki yadda ya kamata. Ficewar da ake cewa 'yan majalisar da ke ƙarƙashin dakatarwa suka yi ba za ta hana Majalisar tafiya da ayyukan taba.


No comments