APC Ta Yi Babban Kamu A Katsina, Shettima Ya Tabbatar Nasarar Dikko Raɗɗa
Daga Hadi Bawa
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya karɓi wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC a jihar Katsina, inda ya bayyana cewa sauya sheƙar na nuna ƙara samun karɓuwar gwamnatin Gwamna Dikko Raɗɗa a tsakanin al’ummar jihar.
TNL HAUSA ta samu rahoton cewa, an gudanar da taron karɓar sabbin ’yan jam’iyyar ne a dandalin People’s Square da ke harabar Gidan Gwamnatin jihar Katsina, a ranar Lahadi, yayin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kai jihar.
Da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayan jam’iyyar, Shettima ya bayyana shigowar ’yan siyasar cikin APC a matsayin ƙarin ƙarfi gare ta gabanin babban zaɓen 2027, yana danganta ci gaban da yadda ya ce gwamnatin Gwamna Raɗɗa ke tafiyar da harkokin jihar.
“Katsina ta Dikko Raɗɗa ce ba ta kowa ba,” in ji Mataimakin Shugaban Ƙasar, yana mai jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba gwamnatin Raɗɗa goyon baya.
Shettima ya yaba wa Raɗɗa kan ayyukan raya jihar da gwamnatinsa ke gudanarwa, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen ƙara samun amincewar jama’a.
Ya kuma buƙaci ’yan jam’iyyar APC su kasance cikin haɗin kai da fahimtar juna da yin aiki tare wajen cimma manufofin jam’iyyar.
A nasa jawabin, Gwamna Raɗɗa ya bayyana sauya sheƙar da ’yan siyasar suka yi a matsayin alamar ƙara samun amincewa da APC da jagorancinta a ƙasa da kuma faɗin jihar Katsina.
Ya ce cikin waɗanda suka koma APC akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, kuma tsohon ɗan takarar Gwamna a APC, Mustapha Muhammad Inuwa; tsoffin ’yan Majalisar Wakilai, Aminu Chindo da Abdul-Aziz Ɗandume; tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Ɓaure, Bala Ɓaure; tsohon mai ba da shawara kan harkokin shari’a na ADC, Barrista Auwalu; da Sallau Arawa, tare da wasu shugabannin jam’iyyun adawa, ’yan majalisu da sauran masu ruwa da tsaki daga PDP, ADC da Action Alliance.
Gwamna Raɗɗa ya ce shigowar waɗannan gaggan ’yan siyasa za ta ƙara wa APC ƙarfi a matakin ƙasa, tare da faɗaɗa tsarin jam’iyyar na tuntuɓar jama’a da magoya baya.
Ya kuma jaddada aniyar APC ta mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a ƙoƙarinsa na neman sake zaɓe a 2027 da kuma samun nasarar ’yan takarar jam’iyyar a faɗin jihar.
Raɗɗa ya kuma bayyana wasu ayyukan Gwamnatin Tarayya da shirye-shiryen tallafi da ake gudanarwa a Katsina, yana mai cewa haɗin gwiwar gwamnatin Shugaba Tinubu da gwamnatin jihar na taimakawa wajen bunƙasa ababen more rayuwa, tattalin arziƙi da shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma.
Shi ma Shugaban APC na Jihar Katsina, Bashir Saulawa, ya danganta yawaitar sauya sheƙar zuwa jam’iyyar da ake samu a waannan lokacin da ayyukan gwamnatin Raɗɗa, tare da tabbatar wa sabbin ’yan jam’iyyar cewa za a ba su dama, kuma a haɗa su cikin tsarin jam’iyyar.
Da yake magana a madadin waɗanda suka sauya sheƙa, Mustapha Inuwa ya bayyana komawarsa APC a matsayin mai da ruwa rijiya, inda ya buƙaci ’yan jam’iyyar su haɗa kai wajen ƙarfafa APC.
Ya ce: “Ba mu da lokacin yin wani abu da zai kawo cikas ga muradunmu na bai ɗaya. Abin da ya kamata mu mayar da hankali a kai shi ne yadda za mu lashe zaɓuka da tabbatar da nasarar APC.”
Inuwa ya kuma tabbatar da biyayyarsa ga Gwamna Raɗɗa, tare da yin kira ga ’yan jam’iyyar da su ci gaba da haɗin kai domin ƙarfafa nasarar APC a jihar Katsina gabanin babban zaɓen 2027.


No comments